Bana tunanin ƴan Nigeria ne: Ɗaliban makarantar Kebbi ta yi ƙarin haske kan ƴan bindiga

Bana tunanin ƴan Nigeria ne: Ɗaliban makarantar Kebbi ta yi ƙarin haske kan ƴan bindiga

  • Wata daliba daga makarantar FGC Birnin-Yauri a jihar Kebbi ta ce bata tunanin maharan da suka kai hari makarantarsu yan Nigeria ne
  • Dalibar ta ce ita da mahaifiyarta sun boye yayin harin sannan ta tabbatar da cewa yan bindigan suka kawo harin
  • Dalibar ta kuma ce yan bindigan sun saki wasu daliban sun kuma tafi da wasu daliban mafi yawanci mata da malamai maza da mata

Wata daliban makarantar FGC Birnin-Yauri a jihar Kebbi wacce ta tsira daga harin a ranar Alhamis ta ce bata tunanin yan bindigan da suka kai hari makarantansu yan Nigeria ne, The Cable ta ruwaito.

A ranar, Alhamis ne yan bindiga suka kutsa makarantar a kan babura suka kuma yi awon gaba da malamai da dalibai da dama.

Dalibai a Makarantar Birnin-Yauri
Dalibai a Makarantar Birnin-Yauri. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindigan da suka kai hari Makarantar Kebbi sun harbi ɗalibai biyu, Shaida

Yayin harin, yan sanda da ke makarantar sun yi kokarin dakile harin amma yan bindigan sun fi su yawa hakan ya yi sanadin rasuwar jami'in dan sanda.

Abin da 'dalibar ta ce game da maharan

Da ta ke magana bayan harin, dalibar makarantar ta ce yan uwanta dalibai da suka jikkata yayin harin a yanzu suna karbar magani.

Rahoton na The Cable ya ce dalibar ta ce yan bindigan sun saki wasu daga cikin daliban amma sun tafi da wasu.

KU KARANTA: 2023: Fastocin neman takarar shugabancin ƙasa na Yahaya Bello sun mamaye Abuja

Ta ce:

"Sun tafi da wasu dalibai. Sun harbi wani dalibi dan ajin karshe. Sun harbi dalibai biyu. Ina tunanin ana musu magani yanzu.
"Sun tafi da daliban SS1 da SS2, mafi yawancinsu mata kuma mutanen (wato yan bindigan) bana tsamanin yan Nigeria ne domin ni da mahaifiya ta mun boye yayin harin."

Harin na Kebbi shine na baya bayan a cikin jerin hare-haren da aka kai a makarantu a arewacin Nigeria.

A wani labarin, kun ji cewa an kashe wani jami'in dan sanda sannan an sace wasu yan kasar China su hudu da ke aiki a layin dogo na Legas zuwa Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa yan bindigan sun labe ne a kan iyakar Adeaga/Alaagba wani gari da ke kan iyakar jihohin Oyo da Ogun a ranar Laraba.

Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga Yan bindigan sanye da bakaken kaftani sun kutsa wurin da ake aikin layin dogon a kauyen Adeaga/Alaagba da ke karamar hukumar Odeda a jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel