'Yan daba sun kutsa cikin kotu sun fatattaki alƙali saboda rikicin sarauta

'Yan daba sun kutsa cikin kotu sun fatattaki alƙali saboda rikicin sarauta

  • Wasu matasa da mata sun kutsa cikin kotu a Warri sun tada zaman kotu saboda rikicin sarauta
  • Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a lokacin da kotun ke fara shirin zaman sauraran karar da aka shigar kan Yarima Tsola Emiko
  • Kungiyar lauyoyi ta Nigeria, NBA, ta yi tir da abin da yan daban suka yi tana mai kira a tsaurara tsaro a kuma yi bincike

Mutane da dama da kungiyoyi sun yi Allah wadai da kutsen da aka yi a babban kotu da ke Warri, da ake zargin ƴan ƙabilar Itsekiri magoya bayan Olu na Warri da aka zaɓa, Yarima Tsola Emiko ne suka yi a ranar Alhamis.

The Nation ta ruwaito cewa lauya mai kare hakkin bil adama, Mr Oghenejabor Ikimi ya yi tir da kutsen da ya kira gidadanci da rashin girmama kotu.

Mutane yayin da yan daba suka kutsa kotu a Warri
Mutane suna watsewa yayin da yan daba suka kutsa kotu a Warri. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun sace 'yan ƙasar waje da ke aikin layin dogo na Legas zuwa Ibadan

Chronicle ta ruwaito cewa 'yan daba da mata sun kutsa cikin kotun suna wakokin yaƙi inda ake sa ran fara sauran ƙarar da aka shigar na kallubalantar zaɓen Yarima Tsola Emiko a matsayin Omoba a ranar na Alhamis.

Ɗan tsohon sarkin (Olu), Ogiame Ikenwoli, Yarima Oyowoli Emiko, kawunsa, Yarima Bernard Emiko da wasu ne suka shigar da karar don kallubalantar zaɓen Yarima Tsola ɗan Ogiame Aluwatse (Olu na 19).

"Kotun na sauraren korafin ne a lokacin da hayaniyar ta ɓarke, ba a ma tsayar da ranar yin shari'ar ba kawai kowa ya watse da rikicin ya barke," wani babban lauya ya bayyana.

Jami'an yan sandan farar hula DSS ne suka fice da Alkalin kotun Jastis V. Akpoje da Cif Efe Akpofure ta kofar bayan kotun.

KU KARANTA: Bana tunanin ƴan bindigan da suka kai hari makarantan mu ƴan Nigeria ne, Ɗaliban Kebbi

An gano cewar kafin a fara zaman kotun, lauyan masu shigar da ƙara Cif Akpofure SAN ya yi magana game da yiwuwar tashin hankali amma wani mai ruwa da tsaki a fadar, wanda shima lauya ne ya bashi tabbacin babu abin da zai faru.

Abin da kungiyar lauyoyi na kasa NBA ta ce

Kungiyar lauyoyi ta Nigeria reshen Warri ta bayyana bakin cikin da mamaki "harin da wasu yan daba suka kai kotun wanda hakan yasa aka dakatar da zaman kotu a ƙarar da aka shigar na kallubalantar zaɓen Olu na masarautar Warri."

Kungiyar ta kuma yi kira ga jami'an tsaro su tsaurara tsaro a kotunan jihar domin kare sake afkuwar hakan kuma a yi bincike don gano wadanda suka kai harin don a hukunta su.

A wani labarin daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya amince da dakatar da ayyukan Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na jihar Zamfara (ZAROTA) bayan yawan koke da ake yi da ayyukan jami'an hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

TVC News ta ruwaito cewa daga yanzu rundunar hadin gwiwa ta yan sanda, VIO, FRSC da jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ne za su rika sa ido kan ayyukan ZAROTA, a cewar sakataren dindindin na ayyukan fadar gwamnati, Yakubu Haidara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel