‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum

‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum

  • Shugaba Buhari ya yi fatan kowane shugaba ya yi koyi da Gwamna Zulum
  • Ya bayyana Gwamna Zulum a matsayin Shugaban da ke sarayar da jin dadinsa domin al’ummarsa
  • Buhari ya matukar nuna jin dadinsa kan gina Cibiyar Koya wa Matasa Sana’o’i

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gagara boye farin cikinsa a ranar Alhamis a Maiduguri bayan da ya kaddamar da ayyuka bakwai cikin 556 da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya aiwatar cikin shekara biyu da ya yi a kan karaga.

Gwamna Zulum da kansa ya bayyana haka a jawabin da ya saki ranar Alhamis a shafinsa.

Buhari yace:

“Ina jin matukar gamsuwa da salon mulkin Mai Girma Gwamna Babagana UMara Zulum yake gudanarwa a Jihar Borno cikin shekara biyun da suka gabata.
‘’Mutum ne ba mai nuna son kansa ba sannan yakan sa kansa cikin hadari domin kawai ya tabbatar da al’ummarsa ta zauna lafiya cikin jin dadi.
‘’Na so a ce duk wani wanda ke jagorantar al’umma a kowane mataki ya yi koyi da Gwamna Zulum maimakon ya tsaya yana ta kame-kame tare da daukar laifinsa ya maka wa wani.

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Gwamna Zulum da Buhari
‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 cikin 556 na Gwamna Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

Buhari ya kara da cewa ce zaga inda na bude wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Zulum ta gudanar cikin shekara biyu tana mulki.

Shugaban ya yi magana kan aiki guda daya tak na Cibiyar Koyar da Sana’o’i wacce ya bude a Muna, inda ya bayyana shi a zaman ‘’Sara a kan gaba da ya zo daidai da bukatar da ake da ita ta koyar da sana’o’i tare da samar da ayyuka’ wanda zai taimaka wajen rage dimbin matasan da ba su da abin yi a jihar da hakan zai hana su shiga ayyukan ta’addanci.

An tsara cibiyar domin koyar da matasa 1,500 a shekara tana da bangaren koyar da sana’ar kanikancin mota da gyaran laturoni da hada wutar sola sarrafa fata da kirgi sana’ar aski da kwalliya da gyaran waya da walda aikin gini da kafinta da harkar fasahar sadarwar zamani da dinki da dai sauran sana’o’i.

Sannan a cibiyar akwai dakunan kwanan dalibai har kimanin 200 da kicin da dakin shakatawa da ofishin gudanarwa da ma wuraren wasanni.

Sauran ayyukan da Shugaba Buhari ya bude sun hada da Jami’ar Jihar Borno wanda gwamnatin Zulum din ta gina.

Shugaban ya kuma bude hanyoyin da gwamnatin jihar a gina a unguwar Jiddari Polo da rukunin farko na gidajen da aka ginawa masu gudun hijira guda dubu 10.

Buhari ya je kwana daya bayan harin da aka kaiwa Sojoji

Wasu masu tayar da kayar baya da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne sun mamaye wani sansanin sojoji a kudancin jihar Borno a ranar Talata sannan suka kwashe makamai bayan wani kazamin artabu da sojojin.

An gano cewa mayakan sun zo cikin motoci kusan 10 domin yin kawanya ga rundunar da aka kafa a kauyen Kwamdi, da ke karamar hukumar Damboa da yammacin ranar Talata.

An ce sun kone manyan makaman soji na 'Ammour Persnal Carrier (APC)' da motar bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel