2023: Ibrahim Shekarau ya bayyana daga yankin da ya kamata APC ta fitar da dan takarar Shugaban kasa

2023: Ibrahim Shekarau ya bayyana daga yankin da ya kamata APC ta fitar da dan takarar Shugaban kasa

  • Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya magantu a kan wanda za a mika wa mulki a 2023
  • Shekarau ya shawarci jam'iyyarsa ta APC da ta mika tikitinta na takarar shugaban kasa ga yankin kudu idan Shugaba Buhari ya kammala wa'adinsa na biyu
  • Ya ce yin hakan shine zai tabbatar da adalci a siyasar kasar

Sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ya kamata jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mulki ta mika wa yankin kudu tikitin takararta na Shugaban kasa a 2023.

A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, Shekarau ya ce akwai bukatar aikata hakan domin tabbatar da adalci da daidaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun

2023: Ibrahim Shekarau ya bayyana daga yankin da ya kamata APC ta fitar da dan takarar Shugaban kasa
Ibrahim Shekarau ya nuna cikakken goyon bayansa ga tsarin mulkin karba-karba Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Da yake magana kan tsarin mulkin karba-karba, Sanata Shekarau ya ce:

“A cikin kundin mulkin APC ba a rubuta batun mulkin karba-karba ba, amma ni na amince akwai tsarin mulki na hankali.
“Misali yanzu tsarin shiyya-shiyya da ake gudanarwa ai ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, amma tsari ne mai inganci, yanzu babu abin da za ka yi ba ka shigo da wannan ciki ba.
"To haka ma lamarin shugabanci tsakanin kudu da arewa, idan aka yi watsi da wannan to gaskiya ba a yi wa juna adalci ba, kuma ba mu yi wa tarihin kafuwar Najeriya adalci ba.
“Ni ina da ra'ayin cewar wajibi ne don kowa ya ji cewar ana yi da shi.”

KU KARANTA KUMA: Jerin gwamnoni bakwai da suka kori masu mukaman siyasa da kuma rusa majalisarsu a 2021

Da aka tambaye shi kan ko yana ganin akwai bukatar mayar da mulki yankin kudu bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu, Shekarau ya ce:

“Sosai ma. Ni ina ganin ya kamata mu yi haƙuri mu jawo ƴan uwanmu na kudu mu da muke daga arewa. Ka ga ai da aka yi zaɓe, arewa ita kaɗai ba za ta yi ƙuri'ar samar da shugaban kasa ba, kudu ita kaɗai ma ba za ta yi ba, sai mun hadu kuma zaman tare muke.
“Ni abin da na yarda da shi shi ne ba ma wai shiyya-shiyya ba, babu wata jiha a Najeriya yau da ba ta da wadanda za su iya yin shugabanci a kasar nan."

Da aka tambaye shi kan ko baya ganin yin hakan zai sa PDP mai adawa tayi galaba a kansu idan ta fito da dan takararta daga Arewa, sai ya ce adalci shine gaba, kuma nagartar wanda aka tsayar shine zai kai ga nasara.

2023: Shugabannin Kudu da Arewa sun yi taro, sun tsaida wadanda za a ba mulki

A wani labarin, The Cable ta ce shugabannin mutanen Kudu da yankin Arewa maso tsakiya na kungiyar SMBLF sun yi taro a ranar Lahadi a game da batun zaben 2023.

A karshen wannan zaman, kungiyar SMBLF ta yarda cewa mulkin kasar nan ya koma Kudu a 2023.

Jagororin kungiyar sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta goyi bayan kiran da al’umma su ke yi na cewa a haramta yawo da dabbobi da sunan kiwo a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel