Da dumi-dumi: INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun

Da dumi-dumi: INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun

  • INEC ta sanar da cewa jihohin Ekiti da Osun za su yi zabukan gwamnoninsu a shekara ta 2022
  • A cewar hukumar zaben, za a gudanar da zaben Osun da Ekiti a ranar 16 ga Yuli da 18 ga watan Yuli bi da bi
  • Ku tuna cewa zabukan da suka gabata a cikin wadannan jihohin sun zo ne da makarkashiya da wasan kwaikwayo da yawa wadanda suka hargitsa kasar

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya ranakun da za ta gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin Ekiti da Osun.

KU KARANTA KUMA: Jerin gwamnoni bakwai da suka kori masu mukaman siyasa da kuma rusa majalisarsu a 2021

Mahmood Yakubu, shugaban INEC, ya bayyana a Abuja ranar Laraba cewa za a gudanar da zaben a Ekiti a ranar 18 ga Yuli, 2022, yayin da na Osun za a gudanar a 16 ga Yuli, 2022.

Da dumi-dumi: INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun
Da dumi-dumi: INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

INEC Ta Soke Wasu Runfunan Zaɓe 746 a Faɗin Najeriya

A wani labarin, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta soke wasu runfunan zaɓe 746 dake faɗin Najeriya, waɗanda mafi yawancin su a wurin bauta, gidan sarauta da kuma wuri mai zaman kanshi suke, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shine ya faɗi haka ranar Laraba a Abuja, a wurin taron da hukumar ke gudanarwa da kwamishinonin zaɓe RECs.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kama matasa 73 tare da babura 47 a hanyarsu ta zuwa jihar Imo daga Nasarawa

Daga runfunan zaɓen 119, 973 da ake da su, Farfesa Yakubu yace yanzun akwai runfunan zaɓe 176, 846 a faɗin Najeriya, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel