2023: Shugabannin Kudu da Arewa sun yi taro, sun tsaida wadanda za a ba mulki

2023: Shugabannin Kudu da Arewa sun yi taro, sun tsaida wadanda za a ba mulki

- Shugabannin kungiyar SMBLF sun yi wani taro jiya a babban birnin Abuja

- Kungiyar SMBLF ta na goyon bayan a kai mulki zuwa Kudu a zaben 2023

- Har ila yau, SMBLF ta na tare da Gwamnonin Kudu a kan hana kiwo a fili

The Cable ta ce shugabannin mutanen Kudu da yankin Arewa maso tsakiya na kungiyar SMBLF sun yi taro a ranar Lahadi a game da batun zaben 2023.

A karshen wannan zaman, kungiyar SMBLF ta yarda cewa mulkin kasar nan ya koma Kudu a 2023.

Jagororin kungiyar sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta goyi bayan kiran da al’umma su ke yi na cewa a haramta yawo da dabbobi da sunan kiwo a Najeriya.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna ya fadawa 'Yan APC, Garba Shehu, su iya bakinsu

Wannan bayanin na su ya na kunshe a cikin takardar da aka fitar a karshen taron da aka gudanar a jiya, ranar 30 ga watan Mayu, 2021, a birnin tarayya Abuja.

Kungiyar ta roki gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbi matsayar da gwamnonin Kudu suka cinma a kan hana kiwo, kiran taron kasa, da sake fasalin kasa.

“Akwai bukatar ayi maza-maza, a canza wa kasar nan fasali saboda halin da aka tsunduma a halin yanzu, kafin zabe mai zuwa.” Inji shugabannin kungiyar SMBLF.

SMBLF ta nemi a rika zagayawa da mulkin kasar nan tsakanin yankin Kudu da Arewacin Najeriya.

2023: Shugabannin Kudu da Arewa sun yi taro, sun tsaida wadanda za a ba mulki
Taron kungiyar SMBLF Hoto: www.thenigerianvoice.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ana zargin Obasanjo da shiryawa Buhari tuggu

“Ana sanar da manyan jam’iyyun siyasa musamman APC da PDP da sauransu cewa idan ana so damukaradiyya ta samu gindin-zama, dole a rika yi da kowa.”

Har ila yau, kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya ta sa dokar ta-baci a kan sha’anin tsaro, sannan a kawo dabarun gaggawa da za su kawo zaman lafiya a Najeriya.

Vanguard ta ce SMBLF ta soki yadda gwamnatin Buhari ta ke daukar matsayar gwamnonin Kudu kan kiwo, a karshe ta ce ana bukatar sabon kundin tsarin mulki.

A jiya ne limamin cocin Christ Revelation Church of God, Fasto Ayodeji Ipinmoroti, ya ce Ubangiji ya nuna masa tsohon Gwamnan Legas zai zama Shugaban kasa.

Fasto Ayodeji Ipinmoroti ya ce Tinubu zai samu mulki, amma wasu abubuwa za su faru kafin ya iya kai ga nasarar. A cewarsa, Ubangiji ne ya nuna masa hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng