Jerin gwamnoni bakwai da suka kori masu mukaman siyasa da kuma rusa majalisarsu a 2021

Jerin gwamnoni bakwai da suka kori masu mukaman siyasa da kuma rusa majalisarsu a 2021

Korar masu rike da mukamai da wasu gwamnoni suka yi kwanan nan na ci gaba da haifar da mabanbantan ra'ayi tsakanin 'yan Najeriya. A makonnin da suka gabata, akalla gwamnoni bakwai ne suka rusa majalisar zartarwarsu ba tare da bayar da dalilan rusa su ba.

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da gwamna Nasir El-Rufai na cikin gwamnonin da suka sauke wasu daga cikin wadanda suka nada kwanan nan.

Don haka Legit.ng ta gabatar da gwamnoni bakwai wadanda ko dai suka sauke wadanda suka nada, ko kuma suka rusa majalisar zartarwarsu a wannan shekarar.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kama matasa 73 tare da babura 47 a hanyarsu ta zuwa jihar Imo daga Nasarawa

Jerin gwamnoni bakwai da suka kori masu mukaman siyasa da kuma rusa majalisarsu a 2021
Gwamna El-Rufai, Okowa da sauransu sun kori wasu daga cikin wadanda suka nada. Hoto: Nasir El-Rufai, Bello Matawalle.
Asali: Facebook

1. David Umahi - Jihar Ebonyi

A watan Mayu, Gwamna David Umahi ya rushe majalisar zartarwar jihar nan take. Umahi ya bayyana cewa za a yi rusan ne a matakai, inda ya nuna mambobi 83 daga cikin 106 na majalisar da abin ya shafa a matakin farko.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa rushewar na da nufin baiwa gwamnati damar gudanar da aikin tantance kokarin su.

KU KARANTA KUMA: Ban mutu ba, Tinubu ya bayyana yayin da ya isa Najeriya daga Dubai

2. Bello Matawalle – Jihar Zamfara

Gwamna Bello Matawalle ya rusa majalisar zartarwa ta jihar nan take. An kuma kori sakataren gwamnatin jihar, shugaban ma’aikata da mataimakin shugaban ma’aikata. Ya kuma sauke dukkan shugabanni da mambobi na kwamitoci da shugabannin hukumomin daban-daban.

3. Ifeanyi Okowa - Jihar Delta

Gwamna Ifeanyi Okowa a cikin watan Mayu, ya rusa majalisar zartarwar jihar jim kadan bayan taron majalisar da ya jagoranta. Okowa ya nemi dukkan kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, shugaban ma’aikata, sakataren gwamnati, babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa da kuma babban mai tsara dabaru da su mika mukamansu ga wadanda ke kusa da su.

Gwamna Okowa ya yaba wa wadanda aka kora

Gwamnan ya godewa dukkan mambobin gwamnatinsa saboda gudummawar da suka bayar wadanda suka kasance a tafiyan cikin shekaru shida da suka gabata da wadanda suka shiga cikin tafiyan a shekaru biyu da suka gabata.

4. Bala Mohammed - Jihar Bauchi

A watan Yuni, Mohammed ya rusa majalisar zartarwar jihar nan take. Ya kuma kori sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Sabiu Baba, shugaban ma’aikata, Ladan Salihu da dukkan masu ba da shawara na musamman.

5. Ben Ayade - Jihar Cross River

Gwamna Ben Ayade a watan Mayu ya kori kwamishinoni hudu daga majalisar sa. Ya kuma sauke wasu mutane biyar da aka nada - Leo Inyambe, Orok Duke, Victor Okon, John Bassey, da Mbeh Agbiji daga mukaminsu.

Duk da cewa bai bayar da wani dalili na matakin nasa ba, amma ya godewa kwamishinonin da wadanda aka nada kan ayyukan da suka yi wa jihar tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da suka sa gaba.

6. Nasir El-Rufai - Jihar Kaduna

Gwamna Nasir El-Rufai a cikin watan Mayu, ya amince da sallamar masu mukaman siyasa 19. Gwamnan ya bayyana cewa ma’aikatan da aka sallama din su ne kashi na farko na ma’aikatan gwamnati da za su bar aikin gwamnati.

7. Hope Uzodimma - Jihar Imo

A watan Mayu ma Gwamna Hope Uzodimma ya rusa majalisar ministocinsa inda ya sauke kwamishinoni 20 daga cikin 28 daga aiki. gwamnan ya ce rushewar ya zama dole ne don sake sauya tsarin da kuma sake ba da karfi ga aiki.

Uzodimma ya godewa kwamishinonin da abin ya shafa kuma ya basu tabbacin cewa har yanzu za a same su masu dacewa a wasu fannoni idan bukatar hakan ta taso, ba su kafa sabuwar majalisa ba.

Gwamnan Bauchi, Bala ya tsige SSG, COS, Kwamishinoni da masu bada shawara

A baya mun kawo cewa, Gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da sanarwar sallamar kusan daukacin kwamishinoni da masu ba gwamna Bala Mohammed shawara.

Kamar yadda sanarwar da ta fito daga ofishin mai taimaka wa gwamnan jihar Bauchi wajen yada labarai da hulda da jama’a, wasu hadimai hudu kacal suka tsira.

Malam Mukhtar Gidado ne ya fitar da takardar wannan sanarwa a shafinsa na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel