Zaben 2023: Babban limami zai shiga tseren neman kujerar gwamna a Adamawa
- Babban limamin masallacin gidan talbijin din jihar Adamawa (ATV), Malam Abdulkadir Isa, ya ce zai yi takarar gwamnan jihar a 2023
- Malam Abdulkadir ya bayyana aniyarsa a yayinda yake zantawa da manema labarai a yau Laraba, 2 ga watan Yuni
- Ya ce zai yi takara ne domin ceto al'umman jihar Adamawa daga halin da suke ciki
Wani labari daga jaridar Aminiya ya nuna cewa babban limamin masallacin gidan talbijin din jihar Adamawa (ATV), Malam Abdulkadir Isa ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar a zaben 2023 mai zuwa.
Malamin ya kasance tsohon ma’aikacin gidan radiyo otel da ke garin Yola, kuma ya kasance mai fatawar addinin Musulunci.
An tattaro cewa malamin ya bayyana kudirinsa ne yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba, 2 ga watan Yuni, a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.
KU KARANTA KUMA: Jama’a na cece kuce yayinda aka tsara katin gayyatar aure kamar takardar kudi N500
Malam Abdulkadir ya ce ko shakka babu a batun tsayawarsa takarar, lamarin da ya ce shine ya sa shi ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar.
Ya ce:
“Kasancewar kowa na da irin tasa fasahar da kuma hangen nesa da karfin zuciya da dogorona ga Allah da kuma bisa wata kaddara da ta sameni ya sanya na yanke shawarar tsayawa takarar Gwamna a jihar.”
Ya kuma nemi mutane da su sanya shi a addu’a, inda yace manufarsa zata farantawa al’ummar jihar rai ba tare da nuna banbancin addini ba da kuma kawo canjin da jihar ke bukata.
Har ila yau, malamin ya ce fitowarsa na bayyana kudirinsa na kokarin ceto al’ummar jihar daga halin da suke ciki.
Ya kara da cewa:
“Na zaga wasu kasashe a duniya na ga yadda talaka yake da daraja. Kuma ni na dauki takarar nan a matsayin ibada zan yi, ma’ana abinda Allah zaiyi sakayya da shi.
“Na sani ba dukkan limami ne ko almajirin ilmi zai iya yunkurin fitowa ba a irin wannan fagen don tsoron maganganun masu magana.”
KU KARANTA KUMA: Cutar taba sigari: Gwamnatin Kano ta haramta shan sigari a cikin jama’a
Daga karshe ya yi kira ga al’ummar jihar da su goya masa baya domin ya kai ga cimma manufarsa.
A wani labari na daban, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yace ba shi da wani shiri na sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a watan Yuni, 12.
Gwamnan yace bai yanke hukunci ko kuma ya tsayar da ranar komawa jam'iyyar APC ba.
A ranar Talata, jaridar Premium times ta ruwaito daga wata majiya dake kusa da gwamnan cewa, Gwamnan ya gama shirye-shiryen ficewa daga PDP a ranar 12 ga watan Yuni, a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da zaiyi a bikin ranar demokaraɗiyya.
Asali: Legit.ng