Jama’a na cece kuce yayinda aka tsara katin gayyatar aure kamar takardar kudi N500
- Jama’a a shafukan sada zumunta sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani katin gayyata na wani daurin aure saboda yadda aka kawata shi
- An tsara katin gayyatar ne kamar takardar kudi na N500 sannan mutane da dama sun zata kudin gaske aka yi amfani da shi
- A cewar mutanen, ci gaba da yada wannan hoto zai jefa angon cikin matsala da hukumomin tsaro
Wani hoton katin gayyatar daurin aure ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan sada zumunta saboda rashin dacewar shi.
An tsara katin gayyatar kamar takardar kudi na N500 kuma mutane da yawa sun sha mamakin abunda idanunsu ya gane masu bayan an yada shi a Twitter.
KU KARANTA KUMA: PDP ta dakatar da shugabanta saboda rashin da’a, ta sanar da madadinsa
Wani mai amfani da @Abdulhamied_AA a Twitter ya saka katin gayyatar a shafinsa. An rubuta a kan katin gayyatar cewa za a gudanar da bikin a ranar Asabar, Yuni 4.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Tawagar motocin ‘dan IBB sun yi hatsari, wasu sun rasa ransu
Ya kamata a sani cewa kudin ba ainihin N500 bane amma wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi tsammanin shine.
Martani ya biyo baya
@ 007Cbia ya ce:
"Wannan bai dacce ba. Za su iya zuwa kurkuku saboda wannan."
@aishaummeey ta yi tsokaci:
"Ba kudin gaske bane. Kawai IV ne aka buga shi kamar takardar naira 500."
@Adamxss ya rubuta:
"Baya bisa ka’ida, ana iya kama su saboda wannan."
@sbzampa ya ce:
"A yi hakuri amma sake yada wannan zai iya sanya Angon cikin matsala kamar yadda za a iya kama shi."
A gefe guda, a wani bidiyo da ya shahara a kafafen sanda zumunta, an ga wani mutum da ya yi ikirarin cewa ya auri aljana kana ya hada ta da matarsa mutum suke zaune a gida daya.
Mijin aljana, wato Malam Ahmadu Ali Kofar Na'isa, ya bayyana wasu abubuwan ban al'ajabi a baya, yayin da yake bayyana yadda yake mu'amalantar matarsa aljana duk da cewa halittarsu daban.
A wani bidiyon, har bayani ya yi na yadda yake cire kudade daga asusun ajiyar aljanu, wanda yake bashi damar cire kudaden Najeriya da wani katin ATM da yake dashi na musamman.
Asali: Legit.ng