Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Yayi Magana Kan Shirinsa Na Sauya Sheƙa Zuwa APC Ranar 12 Ga Yuni
- Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya musanta rahoton cewa yana shirin komawa jam'iyyar APC ranar 12 ga watan Yuni
- Matawalle yace har yanzun bai yanke hukunci ko kuma ya sanya ranar da zai sauya sheƙa ba
- Gwamnan ya kuma musanta zargin cewa matakin da ya ɗauka na sallamar hadimansa yana alaƙa da shirin ficewarsa daga PDP
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yace ba shi da wani shiri na sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a watan Yuni, 12.
KARANTA ANAN: Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa
Gwamnan yace bai yanke hukunci ko kuma ya tsayar da ranar komawa jam'iyyar APC ba.
A ranar Talata, jaridar Premium times ta ruwaito daga wata majiya dake kusa da gwamnan cewa, Gwamnan ya gama shirye-shiryen ficewa daga PDP a ranar 12 ga watan Yuni, a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da zaiyi a bikin ranar demokaraɗiyya.
Matawalle ya zama gwamnan jihar Zamfara ne a 2019 bayan kotun ƙoli ta nesanta APC daga zaɓen da aka yi a jihar saboda jam'iyyar bata gudanar da zaɓen tsaida ɗan takara ba.
An jima ana raɗe-raɗen cewa gwamnan na da kuɗirin sauya sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa APC.
Yayin da yake martani akan wannan rahoton, Mr. Matawalle yace har yanzun bai yanke hukunci akan wannan lamarin ba.
KARANTA ANAN: Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari
Da aka tambayesa ko ya fara tuntuɓar wasu ne kan sauya sheƙarsa da ake ruwaito wa kashi daban-daban? Matawalle yace:
"A matsayina na shugaban siyasa, a koda yaushe ina tuntuɓar mutane da shugabanni a jihar Zamfara bisa wasu manufofin siyasa."
Hakanan kuma gwamnan ya musanta cewa sallamar hadimansa da yayi yana da alaƙa da shirin sauya sheƙarsa.
A cewar gwamnan: "Na sallami hadimaina ne saboda bayan shekara biyu, lokaci yayi da zanyi garambawul a gwamnati na domin fuskantar ragowar Lokaci na."
A wani labarin Kuma Dubbannin Ɗalibai Ka Iya Rasa Damar Zana Jarabawar JAMB 2021, Inji NANS
Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen Kaduna ta nuna rashin jin daɗin ta kan matakin wajabta amfani da profile code wajen yin rijista, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Shugaban NANS na Kaduna, Huzaifa Bello, yace dubbannin ɗalibai ne zasu rasa damar yin jarabawar saboda rashin mallakar lambobin.
Asali: Legit.ng