Cutar taba sigari: Gwamnatin Kano ta haramta shan sigari a cikin jama’a

Cutar taba sigari: Gwamnatin Kano ta haramta shan sigari a cikin jama’a

- An daina barin masu shan sigari a jihar Kano shan sigari a wuraren taruwar jama'a don hana bazuwar cutar taba

- Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya sanar da dakatarwar yayin ganawa da manema labarai

- Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba domin rage yawan masu shan sigari a yankinta

Gwamnatin jihar Kano ta hana shan sigari a wuraren taron jama'a don yaki da cutar sigari yayin da Najeriya ke kiyasta fiye da mutane 16,100 da ke mutuwa a kowace shekara saboda cututtukan da ke da alaƙa da shan sigari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an sanar da hukuncin ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin, 31 ga watan Mayu, a ma’aikatar lafiya ta Kano don bikin ranar hana shan taba sigari ta Duniya.

KU KARANTA KUMA: Jama’a na cece kuce yayinda aka tsara katin gayyatar aure kamar takardar kudi N500

Cutar taba sigari: Gwamnatin Kano ta haramta shan sigari a cikin jama’a
Cutar taba sigari: Gwamnatin Kano ta haramta shan sigari a cikin jama’a Hoto: @GovUmarGanduje
Asali: UGC

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya sanar da haka kuma ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki ba tare da gajiyawa ba domin rage yawan masu shan sigari da kuma yawan shan sigari a jihar.

Ya ce:

“Muna da dokar hana shan taba a cikin jama’a da sayarwa yara ‘yan kasa da shekara 18.”

Ya kara da cewa gwamnatin za ta kara himma wajen wayar da kan al’umma su fahimci hadarin da ke tattare da zukar hayakin taba da dalilin da ya sa ya kamata su daina shan tabar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Tawagar motocin ‘dan IBB sun yi hatsari, wasu sun rasa ransu

A cewarsa, gwamnatin ta mayar da hankali sosai tare da kashe makudan kudade wajen yaki da cututtukan da ba a daukar su da suka hada da cutar hawan jini da asma da ciwon huhu da kansa da sauransu.

Kwamishinan ya kara da cewa zuwa yanzu akwai doka a gaban Zauren Majalisar Jihar a kan kafa hukumar da za ta kula da hana shan miyagun kwayoyi wanda ake son kafawa da zimmar rage harkar shaye-shaye a tsakanin al’ummar jihar.

Abdul Rabbi ya rubuta:

“Wannan daidai yake da hana shan ruwa a bainar jama’a, don haka ka manta da gwamnan ba haka yake nufi ba. Yana wasa ne."

Alee Abdallah ya rubuta:

"Na yaba wa gwamnan kan hakan."

Sunusi Sani ya rubuta:

“Yunkuri mai kyau. Abu na gaba shi ne gwamnati ta dauki tsauraran matakai wajen tunkarar masu satar waya. Suna shagalta da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba don kwace kayansu !!!"

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nada daraktan fina-finai, Ishaq Sidi Ishaq mai bashi shawara na musamman.

Kamar yadda takardar nadin ta nuna, Ganduje ya nada Ishaq ne matsayin babban mai masa hidima ta harkokin kirkira wato Creative Industry.

Sanannen daraktan fina-finai, Falalu Dorayi ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi inda yake cewa: "Muna taya darakta Ishaq Sidi Ishaq murnar samun mukamin babban mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a fannin kirkira."

Asali: Legit.ng

Online view pixel