Mutumin da ya kai wa Limamin Harami hari ya ce shi ne Mahdi

Mutumin da ya kai wa Limamin Harami hari ya ce shi ne Mahdi

- Mutumin da ya yi yunkurin halaka Limamin Masallacin Harami ranar Juma’a ya yi ikirarin cewa shi ne Mahdi

- Mutumin ne ya yi ikirarin hakan ne a yayinda yan sanda ke tuhumarsa

- Hukumomin da ke sanya idanu a kan Masallacin Harami ne suka sanar da ci gaban

Mutumin da ya yi yunkurin kai wa Limamin Masallacin Ka’aba da ke birnin Makkah hari a yayinda yake gabatar da hudubar sallar Juma’a, a ranar 21 ga watan Mayu, ya yi ikirarin cewa shi Mahadi ne.

Hukumomin da ke sanya idanu a kan Masallatai biyu masu tsarki na kasar Saudiyya wato Haramain Sharifain sun bayyana cewa maharin ya yi kokarin halaka Limamin, Sheikh Bandar Baleelah a yayinda yake hudubar.

Haramain Sharifain ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, mutumin wanda ɗan ƙasar Saudiyyan ne mai shekara 40, ya yi ikirarin cewa shi Imamu Mahdi ne.

Mutumin da ya kai wa Limamin Harami hari ya ce shi ne Mahdi
Mutumin da ya kai wa Limamin Harami hari ya ce shi ne Mahdi Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ku yi ku gama: Sabon tsarin APC ba zai hana Tinubu zama shugaban ƙasa a 2023 ba, cewar wani jigo

Ya bayyana hakan ne a lokacin da jami’an tsaro na yan sanda ke tuhumarsa. Sai dai hukumar ba ta yi karin bayani kan matakin da aka dauka a kansa ba.

Imamu Mahadi shi ne wani mutum da wasu Musulmai suka yi imanin cewa zai zo a karshen duniya.

Haramain Sharifain ya wallafa bidiyon a shafinsa na sada zumunta yadda mutumin ya yi yunkurin afkawa ga limamin da kuma yadda jami'an tsaro suka damke shi

KU KARANTA KUMA: Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane a kan lamarin:

@Sol_MDMec ya ce:

"Wadannan mutanen, hakan ya sanar da kai bai san komai ba game da addininsa, Hadisi ya ce, Mahadi, bai san shi Mahadi bane kuma ba zai so ya zama ba. Amma har yanzu kowani mahaukacin zai zo ya ce shi ne. Allah Ya kiyaye mu."

@MohamedRashido1 ta yi martani:

"Ko Mahadi idan ya bayyana ba zai san shi Mahadi ba ne, Allah Subhanauhu Wa Thaala ne kawai ya san lokacin da zai bayyana."

@saaxir ya ce:

"Mashaa Allah… kun ga yadda tsamurarren mai tsaron ya murkushe babban mai kutsen? Masha Allah ya kamata limamin ya ba mai gadin tukwici."

A baya mun kawo cewa a ranar Jumu'a yayin gudanar da huɗuba, wani mutumi sanye da harami yayi ƙoƙarin hallaka ɗaya daga cikin limaman masallacin Ka'aba.

Mutumin yayi ƙoƙarin isa ga limamin amma sai jami'an tsaro suka farga kuma suka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel