Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah

Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah

- Rahotanni daga ƙasar Saudiyya na nuni da cewa wani mutumi yayi yunƙurin kashe limamin ka'aba ranar Jumu'a

- Hukumar dake kula da masallatai biyu masu daraja a ƙasar ce ta bayyana haka a shafinta na kafar sada zumunta.

- Hukumar tace mutumin ya tunkari munbarin da limamin ke huduba ɗauke da makami amma jami'an tsaron suka murƙushe shi

Rahotanni sun bayyana cewa a jiya Jumu'a yayin gudanar da huɗuba, wani mutumi sanye da harami yayi ƙoƙarin hallaka ɗaya daga cikin limaman masallacin Ka'aba.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Katsina Ya Tunɓuke Rawanin Wani Hakimi Bayan Gano Yana Taimakawa Yan Bindiga

Mutumin yayi ƙoƙarin isa ga limamin amma sai jami'an tsaro suka farga kuma suka kama shi.

Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah
Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah Hoto: bbc.com/hausa
Asali: Twitter

Hukumar dake kula da manyan masallatai biyu masu daraja 'Haramain Sharifain' ita ce ta bayyana haka a shafinta na kafar sada zumunta Facebook.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Amurka Tayi Magana Kan Kashe Abubakar Sheƙau, Tace Ba Zata Baiwa ISWAP Tukuici Ba

Hukumar tace anyi yunƙurin kashe Sheikh Baleelah a dai-dai lokacin da yake huɗubar sallar jumu'a a masallacin ka'aba.

Hakanan hukumar Haramain Sharufai ta sanya bidiyon yadda mutumin yayi ƙoƙarin kutsawa zuwa ga limamin da yadda jami'an tsaro suka yi gaggawar damƙe shi a shafinta na kafar sada zumunta.

A jawabin da hukumar tayi tace: "Wani mutumi ya tunkari inda mumbarin liman yake a masallacin ka'aba riƙe da makami, amma jami'an tsaro sun yi nasarar damƙe shi."

A wani labarin kuma IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu

Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, yace babu wani abun tsoro kan barazanar kawo hari Abuja da Plateau.

Ya roƙi jama'ar dake zaune a Abuja da jihar Plateau su kwantar da hankalinsu kuma su cigaba da tafiyar da rayuwarsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel