Ku yi ku gama: Sabon tsarin APC ba zai hana Tinubu zama shugaban ƙasa a 2023 ba, cewar wani jigo

Ku yi ku gama: Sabon tsarin APC ba zai hana Tinubu zama shugaban ƙasa a 2023 ba, cewar wani jigo

- Shirye-shiryen da ake yi don tabbatar da tikitin takarar shugaban kasa na APC ya zamo a bude ga dukkan yan takarar na ci gaba da haifar da cece-kuce

- Kodayake, da yawa daga cikin jiga-jigan jam'iyyar sun ki amincewa da matakin, suna masu cewa wani shiri ne na tursasa dan takarar arewa a jam'iyyar

- Wani jigo a jam'iyyar daga jihar Kaduna ya ce matakin ba zai shafi kudirin son zama Shugaban kasa na Asiwaju Bola Tinubu ba

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna, Alhaji Muhammadu Murtala ya ce shawarar da jam’iyyar ta yanke na bude tikitin takararta na shugaban kasa a 2023 ba zai shafi kudirin shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba.

Tinubu, babban jigon jam’iyya mai mulki ta APC na kasa na daya daga cikin wadanda ke kan gaba wajen neman tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023.

KU KARANTA KUMA: Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari

Ku yi ku gama: Sabon tsarin APC ba zai hana Tinubu zama shugaban ƙasa a 2023 ba, cewar wani jigo
Ku yi ku gama: Sabon tsarin APC ba zai hana Tinubu zama shugaban ƙasa a 2023 ba, cewar wani jigo Hoto: @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

Murtala, babban mai goyon bayan Tinubu a yankin arewa maso yammacin kasar, ya yi wannan bayanin ne yayin tattaunawa da jaridar Daily Trust.

Ya ce ya kamata shugabannin jam’iyyar su bi tsarin karba-karba inda ake sa ran za a mika mukamin shugaban kasa zuwa yankin kudancin kasar da nufin tabbatar da adalci da gaskiya.

Kalaman nasa:

"Cif Tinubu ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ta hanyar doka kuma abin da ake kira bude tikiti ba zai dakatar da shi ba."

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta gabatar a baya ya bayyana cewa tuni aka samu rudani a cikin APC kan sanarwar da gwamnonin jam’iyyar suka yi kwanan nan cewa tikitin takarar shugaban kasa na 2023 a bude yake ga dukkan mambobin da ke da sha’awa.

A cewar rahoton, ana cece-kuce game da tsarin karba-karba na tikitin takarar shugaban kasa tsakanin arewa da kudu gabanin takarar shugaban kasa ta 2023.

Tuni, wasu gwamnonin APC da sauran jiga-jigan jam'iyyar daga kudu, ba su gamsu da ci gaban ba, domin tuni aka fara korafi kan cewa babu wani taron hukuma na shugabannin zartarwar a hukumance inda aka tattauna sosai kan batun karba-karba da yanke shawara.

A wani labarin, kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba zai nemi zarcewa zango na uku a cikin ofis ba, kuma baya sha'awar yin hakan.

A cewar Mr, shehu, wanda ya tattauna da gidan talabishin na Arise tv ranar Talata, Shugaban ƙasa yana matuƙar damuwa kan hare-haren da ake kaiwa ofisoshin INEC da caji ofis ɗin yan sanda kuma ƙona su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Shugaban ya bayyana masu hannu a waɗannan hare-haren a matsayin masu son kawo tashin-tashina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel