Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari

Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari

- Kungiyar Dattawan Arewa ta ce kudu ta hadewa arewa kai a Najeriya

- Kungiyar ta koka kan yadda shugabannin siyasa a kudancin Najeriya ke rura wutar rarrabuwa tsakanin kabilu ta hanyar kalamansu da ayyukansu

- Ta yi zargin cewa hakan suna faruwa ne saboda gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta nuna gazawar shugabanci

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta zargi shugabanni a yankunan kudancin Najeriya da hadewa arewa kai.

Kungiyar ta koka kan yadda lamarin ya sanya fargaba a zukatan ‘yan Arewa, musamman Fulani da ke zaune a sassa daban-daban na kasar, jaridar Nigerian Tribune ra ruwaito.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya Na Bukatar 'Yan Siyasa Masu Hankali, Gwajin Shan Kwayoyi Ya Zama Dole, NDLEA

Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari
Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Kakakin NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 25 ga Mayu, ya yi ikirarin cewa shugabannin kudu maso gabas a yanzu suna kullawa gwamnatin tarayya tuggu da kiraye-kirayen ballewa.

Dangane da yankin kudu maso yamma, Baba-Ahmed, ya yi zargin cewa shugabannin yankin sun karfafa gwiwar ‘cin zarafi na kabilanci’ don tilasta wa gwamnatin tarayya yin abin da suke so.

Kungiyar ta koka kan yadda zababbun jami’ai a kudancin Najeriya a yanzu suke nuna halin ko in kula da dabi’ar neman ballewa.

KU KARANTA KUMA: Mako Ɗaya Bayan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru, Rundunar Soji Ta Shirya Gagarumin Bikin POP

NEF ta kuma zargi gwamnonin kudu da fakewa a karkashin inuwar kabilanci wajen yin kalaman son zuciya don samun rangwame.

Kungiyar ta ce kungiyar gwamnonin kudu ce ke kirkirar ra'ayi da ke nuna cewa dukkan kudu na adawa da fadar shugaban kasa da kuma Fulani makiyaya, The Sun ta ruwaito.

Har ila yau, ta lura cewa wannan matakin da gwamnonin kudu suka dauka ya biyo bayan raunin shugabancin kasa da kuma rugujewar tsarin siyasa.

Wani bangare na bayanin da Legit.ng ta gani ya ce:

“Mummunar halayyar fadar shugaban kasa game da jawo ‘yan Najeriya don shiga cikin batutuwa, korafi, da kuma rashin sanar da cikakken bayani ga yawancin ‘yan kasa wadanda ke nufin alkhairi, a karkashin halin da muke ciki yanzu, yana da hadari.

“Yana bukatar Shugaba Buhari ya tabbatar da karfin da kundin tsarin mulkinmu ya ba shi don kare mutuncin yankinmu da kuma kare yan kasa, ko kuma ya yarda cewa ba shi da ikon jagorantar kasar nan ta hanyar wadannan kalubalen da ba a taba gani ba.

"Idan kasarmu ta iya tsallake matsalolin da take ciki a yanzu kuma ta gina kasa mai inganci, dole ne Shugaba Buhari ya inganta matakan kwarewarsa, wayar da kan jama'a cewa kasar na fadawa cikin bala'i, da kuma lura da damuwar 'yan Najeriya."

Sai dai kungiyar ta sake maimaita shirinta don bincikar ingantattun hanyoyi zuwa kyakkyawar makoma.

A wani labarin, mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi karin-haske a game da kudin satar da ta ke karbowa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya na cewa ayi wa ‘Yan Najeriya bayanin abin da aka karbo, da inda aka kai kudin.

Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya yi wannan jawabi ne a garin Sokoto a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, 2021, yayin da yake magana a wajen wani taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel