'Yan Najeriya Na Bukatar 'Yan Siyasa Masu Hankali, Gwajin Shan Kwayoyi Ya Zama Dole, NDLEA

'Yan Najeriya Na Bukatar 'Yan Siyasa Masu Hankali, Gwajin Shan Kwayoyi Ya Zama Dole, NDLEA

- Hukumar NDLEA ta saake jaddada bukatar yi wa daliban jami'a da 'yan siyasa gwajin kwayoyi

- Hukumar ta dage cewa, akwai bukatar 'yan Najeriya su ba da amanar baitul malinsu ga masu hankali

- Hakazalika, gwajin zai shafi bangarori da dama na cudanyar aiki da siyasa a fadin Najeriya inji hukumar

Shugaban Hukumar hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayyana bukatar ‘yan siyasa da ke neman ofisoshin gwamnati da daliban manyan makarantu a yi musu gwaji na tabbatar da basa shan kwayoyi.

A cewar wata sanarwa daga Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, shugaban NDLEA din ya yi magana ne a ranar Talata a Abuja yayin da yake gabatar da takarda kan ‘Shaye-shayen miyagun kwayoyi da tsaron kasa: Samar da mafita’, The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta nakalto Marwa na jaddada bukatar 'yan siyasa su yi gwajin shan kwayoyi yayin da zabe ke karatowa a wasu jihohi da kuma fadin kasar.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Ci Bashin Da Ya Fi Karfin Kaduna, Ko Jikoki Ba Za Su Iya Biya Ba, Inji PDP

'Yan Najeriya na bukatar 'yan siyasa masu hankali, gwajin shan kwayoyi ya zama dole, NDLEA
'Yan Najeriya na bukatar 'yan siyasa masu hankali, gwajin shan kwayoyi ya zama dole, NDLEA Hoto: live.mrf.io
Asali: UGC

“Shugaban Hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohamed Marwa (mai ritaya) ya sake jaddada bukatar 'yan siyasa masu neman ofis din gwamnati da daliban da ke neman shiga manyan makarantu su yi gwajin kubuta daga miyagun kwayoyi” in ji sanarwar.

Ya ce akwai bukatar mutane su ba da amanar gudanar da baitul malinsu da jin dadinsu a hannun ‘yan siyasa masu hankali.

Ya bayar da hujjar cewa babu wani mai rike da mukamin gwamnati da ke cikin maye da zai iya yin tunanin ci gaba.

Marwa ya ce irin wannan lamari ya shafi daliban da ke neman shiga manyan makarantu a fadin kasar.

Ya ce saboda hujja mai karfi da ke tsakanin shaye-shayen miyagun kwayoyi da kalubalen tsaro a duk fadin kasar, dole ne a hada karfi da karfe don shawo kan matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi kai tsaye.

Ya ce, “Game da wannan, muna yin iya kokarinmu a bangarenmu na hukumar NDLEA. Akwai canjin yanayi a tsarin mu na fuskantar abubuwan maye.

A baya cikin watan Janairu, Marwa ya ce zai gabatar wa da gwamnati bukatar gwajin shan kwayoyi ga dukkan manyan makarantun gaba da sakandare, The Guardian ta ruwaito.

Ya kara da cewa za a kuma gudanar da gwajin ne ga mambobin bautar kasa (NYSC), sabbin ma’aikata, dukkan hukumomin tsaro, sabbin daukar ma’aikata, da kuma gwajin ba zata ga wadanda gwamnati ta nada mukamai.

KU KARANTA: CSO Ta Yi Fatali da Kudurin Soke NYSC, Ta Bayyana Dalilanta

A wani labarin, Hukumar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta hada wani kwamiti da zai binciki hadurran jirgin sama da ke ci gaba da faruwa.

Wannan na zuwa ne a cikin damuwar da ‘yan Najeriya suka nuna biyo bayan hadarin jirgin sama uku da ya faru a cikin watanni uku.

Hadarin ya haifar da asarar rayukan jami'an sojoji 18, ciki har da na makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban hafsan sojin Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru, Vanguard News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel