El-Rufai Ya Ci Bashin Da Ya Fi Karfin Kaduna, Ko Jikoki Ba Za Su Iya Biya Ba, Inji PDP

El-Rufai Ya Ci Bashin Da Ya Fi Karfin Kaduna, Ko Jikoki Ba Za Su Iya Biya Ba, Inji PDP

- Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin El-Rufai a Kaduna da runtumo bashin da ya fi karfinta

- Jam'iyyar ta ce, bashin da gwamnan ya ci babbar barazana ne ga masu tasowa nan gaba a jihar ta Kaduna

- Jam'iyyar PDP na ci gaba da kakaba zargi kan gwamnatocin jam'iyya mai ci ta APC kan lamura da dama

Babbar jam`iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin jihar Kaduna karkashin Mallam Nasiru El-Rufai da jefa makomar al`ummar jihar cikin hadari ta hanyar cin bashin da zai iya zama barazana ga al`ummomi masu tasowa.

Jam`iyyar PDP ta ce a cikin shekaru shida da suka wuce, gwamnatin APC mai mulki a jihar ta ci bashin da ya kai N170bn, kuma babu wani abin a zo a gani na wannan kudin.

PDP dai ta yi zargin cewa babu ranar biyan bashin amma tuni jam`iyyar APC ta musanta zargin.

A cewar Manjo Yahaya Ibrahim Shunku mai ritaya, jigo a PDP ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin El Rufa'i kadai ta karbi bashin $341m a shekarar 2020.

KU KARANTA: Majalisar Wakilai Na Duba Yiwuwar Soke Bautar Kasa ta NYSC Kwata-kwata a Najeriya

El-Rufai Ya Runtumo Bashin Da Ko Jikoki Ba Za Su Iya Biya Ba, Inji PDP
El-Rufai Ya Runtumo Bashin Da Ko Jikoki Ba Za Su Iya Biya Ba, Inji PDP Hoto: bbc.com
Asali: UGC

"Lokacin da wannan gwamnati ta APC ta zo a shekara ta 2015, ana bin jihar Kaduna bashin sama da $226m- kusan gwamnoni 15 kafin zuwan wannan gwamnati." in ji Shunku.

PDP dai ta nemi gwamnatin ta Kaduna ta fito ta yi wa jama'a bayani kan abin da yake faruwa kafin lokaci ya kure.

Sai dai APC a martaninta ta ce abin da PDP take ba abin mamaki bane face adawa kawai.

Sakataren APC a Kaduna, Yahaya Baba Pate ya ce "abokin adawa ai kullum ba zai yi maka adalci ba saboda mutanen jihar sun san cewa gwamnati ta ciyo bashin domin ci gaban al'umma."

Ya ce al'ummar jihar Kaduna suna ganin amfanin bashin wajen gyare-gyaren tituna da asibitoci da kuma makarantu.

Jam'iyyar PDP dai na ci gaba da zarge-zargen gwamnatocin APC ta fuskoki da dama kan lamuran mulki da kuma halin da kasar nan ke ciki.

A makon, jam'iyyar PDP ta kuma zargi jam'iyya mai ci ta APC da shirya manakisar kone-konen ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC don kawai ta cimma burin kassara zaben shekara ta 2023 mai zuwa nan gaba, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ganin yawaitar kone-konen ofisoshin yasa babbar jam’iyyar adawar ta dage cewa jam’iyya mai mulki “tana tallata ayyukan tarzoma ciki har da kona ofisoshin INEC a wasu don kawo yanayin gaggawa da kuma kawo cikas ga yadda za a gudanar da babban zabe na 2023.”

KU KARANTA: CSO Ta Yi Fatali da Kudurin Soke NYSC, Ta Bayyana Dalilanta

A wani labarin, Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ayuba Wabba, ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da yin hayar 'yan daba cike da manyan motoci 50 domin su fatattaki ma'aikata masu zanga-zanga a jihar.

Wabba ya bayyana hakan ne da safiyar ranar Laraba, 18 ga watan Mayu yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, a shirin Sunrise Daily.

Wabba ya zargin gwamnan jihar da biyan N500 ga kowane matashi domin kawo hargitsi a in da ma'aikata ke zanga-zangar korar adadi mai yawa na ma'aikatan gwamnati da jihar ta yi a ranar Talata, 18 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel