CSO Ta Yi Fatali da Kudurin Soke NYSC, Ta Bayyana Dalilanta

CSO Ta Yi Fatali da Kudurin Soke NYSC, Ta Bayyana Dalilanta

- Cibiyar tabbatar da adalci da nuna gaskiya sun yi Allah wadai da sabon kudirin soke kungiyar bautar kasa ta matasa

- Kungiyar ta ce kururuwar dakatar da NYSC wani mummunan shiri ne akan matasan Najeriya baki daya

- A cewar kungiyar, NYSC ta fi kowa kokarin hada kan ‘yan Najeriya duba da yadda aikinta yake gudana

Wata kungiyar farar hula, Center for Social Justice, Equity and Transparency (CESJET), ta yi Allah wadai da bijiro da wani kudiri na soke aikin bautar kasa na NYSC, da wani dan majalisar wakilai ya yi.

CESJET ta ce dokar da ke ba da shawarar dakatar da NYSC wani mummunan shiri ne ga matasan Najeriya. Kungiyar ta ce tunanin soke NYSC, ya samu goyon baya ne daga wakilai masu son hargitsa Najeriya.

Da yake magana a wani taron manema labarai wanda wakilin jaridar Legit.ng ya halarta a Abuja a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, babban sakataren CESJET, Isaac Ikpa, ya ce ba za a iya kwatanta muhimmancin shirin ga Najeriya ta yanzu ba.

KU KARANTA: Ku Sake Shi Yanzu: Gwamnatin Buhari Ta Yi Allah Wadai Da Tsare Shugaban Kasar Mali

CSO Ta Ki Amincewa Da Kudurin Soke NYSC, Ta Bayyana Dalilanta
CSO Ta Ki Amincewa Da Kudurin Soke NYSC, Ta Bayyana Dalilanta Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ikpa ya lura cewa babbar manufar NYSC ita ce sasantawa da sake hada kan ‘yan Najeriya bayan yakin basasa, wanda kuma soke shi a yanzu zai cutar da zaman lafiya, tsaro da hadin kan kasar.

Ya ce dubban matasa ‘yan Najeriya da suka kammala karatu har yanzu suna fatan shiga tsarin na tilas na shekara daya kuma NYSC na ci gaba da dinke barakar da ke tsakanin kabilun Najeriya da addinai.

Ya kara da cewa shirin ya inganta ruhin kishin kasa a Najeriya, Ikpa ya ce, an bai wa matasa dama na dogaro da kai a shirye-shiryen rayuwa ta hanyar alawus-alawus da ake biyansu da kuma gogewar NYSC.

A madadin CESJET, Ikpa ya bukaci shugabannin majalissar dokokin kasar da su sanya bukatun kasar a cikin zuciya tare da dakatar da ci gaba da tattaunawa a kan babban kudurin da ba shi da cikakken bayani.

KU KARANTA: Rundunar Sojin Sama Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Hadurran Jirgin Sama a Najeriya

A wani labarin, Majalisar Wakilai na duba yiwuwar dakatar da shirin bautar Kasa na NYSC, jaridar Punch ta ruwaito.

Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na Canji shekarar 2020, wanda ke neman soke dokar NYSC, an gabatar da shi a karatu na biyu.

Wanda ya dauki nauyin yunkurin, Mista Awaji-Inombek Abiante, a cikin bayanin shawarar, ya zayyana dalilai daban-daban da za su sa a soke NYSC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel