Rundunar Sojin Sama Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Hadurran Jirgin Sama a Najeriya
-Rundunar sojin saman Najeriya ta kafa kwamiti don binciken hadurran jiragen sama a Najeriya
- Rundunar ta bayyana damuwarta da yawaitar hadurran jirgin sojin saman Najeriya a shekarar nan
- Kwamitin zai yi aiki ta fuskoki da dama don tabbatar da binciken kwa-kwaf kan lamarin hadurran
Hukumar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta hada wani kwamiti da zai binciki hadurran jirgin sama da ke ci gaba da faruwa.
Wannan na zuwa ne a cikin damuwar da ‘yan Najeriya suka nuna biyo bayan hadarin jirgin sama uku da ya faru a cikin watanni uku.
Hadarin ya haifar da asarar rayukan jami'an sojoji 18, ciki har da na makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban hafsan sojin Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru, Vanguard News ta ruwaito.
KU KARANTA: Gwamna Zulum Na Jihar Borno Ya Yi Garambawul Ga Kwamishinonsa
Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce kwamitin da Shugaban Hafsun Sojojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao ya kafa, ya kunshi ma’aikatan da suka yi ritaya.
Gabkwet ya bayyana cewa mambobin kwamitin za su gudanar da binciken lafiya na dukkan sassan NAF na aiki da injiniyoyi, ya kara da cewa CAS ta umarci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa kafin 18 ga watan Yuni, 2021.
A cewarsa, mataimakin kwamandan rundunar Operation HADIN KAI, Air Vice Marshal Abraham Adole ne zai jagoranci kwamitin, Daily Trust ta ruwaito.
"Kwamitin zai kuma yi aiki tare da rukunin masu aiki da ma'aikatan fasaha don ra'ayoyi, abubuwan lura da gudummawa kan matakan tsaro," sanarwar ta karanta.
KU KARANTA: Badakalar Ibori: An Tura £4.2M da Aka Kwato Zuwa Jihar Delta, Akanta-Janar
A wani labarin, Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Litinin ya umarci sojoji da su daina jin zafi game da mutuwar Shugaban hafsan sojoji, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10 a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a.
Da yake jawabi a gidan Attahiru da ke Abuja yayin addu’o’in kwana uku na Fidau, CDS ya bukaci sojojin su ci gaba da kasancewa masu kwarin gwiwa tare da mai da hankali kan matsayinsu na tsarin mulki, Daily Trust ta ruwaito.
“Sako na ga mambobin rundunar sojojin Najeriya shi ne cewa su ci gaba da jajircewa tare da kwazo kan matsayin su na tsarin mulki a wannan lokacin jarrabawa. Bai kamata karsashinsu yayi sanyi ba game da lamarin da ya faru,'' inji Irabor.
Asali: Legit.ng