Eidul Fitr: Bayan Ramadan, Ya Kamata Mu Ninka Ayyukan Mu, Bola Tinubu

Eidul Fitr: Bayan Ramadan, Ya Kamata Mu Ninka Ayyukan Mu, Bola Tinubu

- Jagoran jam'iyya mai mulki APC, Bola Tinubu, ya roƙi musulmi da su ƙara ninka ayyukansu fiye da yanda suke yi a baya

- Jagoran yace kada yan Najeriya su mance da darussan da suka koya a yayin azumin watan Ramadana

- Ya kuma roƙi musulmai da yan Najeriya da su saka shugaban Ƙasa Buhari da jami'an tsaro a cikin addu'o'in su.

Jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya roƙi musulmi yan Najeriya da su ƙara zage dantse bayan wucewar watan azumin Ramadana, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗan Sanda a Wani Sabon Hari a Jihar Akwa Ibom

Tinubu, a sakonshi na taya murnar Eidul Fitr 2021, wanda aka yiwa take da "Aiki nagari, ƙoƙarin da muka yi a ramadan ya wuce haka nan gaba" yayi kira ga musulmi da kuma yan Najeriya baki ɗaya da kada su watsar da darasin da suka ɗauka a azumin wata ɗaya da suka yi.

Tinubu Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu da Yakamata Musumai Su Yi Bayan Kammala Ramadan
Tinubu Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu da Yakamata Musumai Su Yi Bayan Kammala Ramadan Hoto: @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

A cewarsa, Ramadan yana koyar da soyayya da tausayawa juna, sabida haka ya kamata musulmi su cigaba da nuna soyayya da tausayi ga maƙotansu.

Tinubu yace: "A yanzu da watan azumin ramadan yake ƙarewa, ya kamata mu tunasar da kanmu kada mu watsar da darasin dake cikinsa, mu ninka abinda muke yi a baya, mu rinka tausayin junan mu da fahimtar juna."

KARANTA ANAN: Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed

"Ya zama wajibi mu gina al'ummar da muke rayuwa da ita, mu kare ta daga tashin hankali da ƙiyayya."

"Kada mu ɗauki magan-ganun wasu da zasu saka gaba tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa, ɗan Najeriya da ɗan Najeriya."

Tsohon gwamnan jihar Lagos ɗin ya kuma roƙi yan Najeriya da su yiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari addu'a ya samu ƙwarin guiwar tafiyar da ƙasar nan kan hanyar da ta dace.

Hakanan ya roƙi yan Najeriya su yiwa jami'an tsaron ƙasar nan dake filin yaƙi addu'a kan Allah ya basu nasara akan yan bindiga da mayaƙan Boko Haram.

A wani labarin kuma Ba Zamu Bar Yan Adawa Suga Bayan Shugaba Buhari ba, Gwamnan APC

Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaƙ yace bai kamata gwamnonin APC su zura ido suna gani yan adawa na ƙoƙarin cutar da shugaba Buhari ba.

Gwamnan yace mafi yawancin gwamnonin da farin jinin shugaban suka samu damar ɗarewa mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel