Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗan Sanda a Wani Sabon Hari a Jihar Akwa Ibom
- Wasu yan bindiga sun hallaka wani ɗan sanda a wani sabon hari da suka kai jihar Akwa Ibom
- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kai harin ne a wasu ofisoshin hukumar yan sanda dake ƙaramar hukumar Etim Ekpo
- Kakakin rundunar yan sanda na jihar, SP Odiko Macdon, ya tabbatar da kai harin amma yace hukumomi na ɗaukar mataki akan lamarin
Yan Bindiga sun hallaka ɗan sanda a wani sabon hari da suka kai ofisoshin yan sanda biyu a ƙaramar hukumar Etim Ekpo jihar Akwa Ibom.
KARANTA ANAN: Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa
Rahoton Dailytrust ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Laraba.
A jawabin kakakin hukumar yan sanda, SP Odiko Macdon, yace yan bindigan sun fara kai hari ofishin yan sanda dake Etim Ekpo, inda suka hallaka ɗan sanda mai suna, Edogi Bassey.
Daga baya kuma sai suka karasa ofishin yan sanda dake Ika, Odiko Macdon Yace:
"Da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar yau, wasu mutane ɗauke da bindigu ƙirar AK-47 da wasu muggan makamai, suka kai hari a jerin wasu gidajen haya a Etim Ekpo da kuma ofishin yan sanda dake wurin."
KARANTA ANAN: Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC
"jami'an tsaron dake aiki a ofishin, sun maida martani tare da fatattakar maharan. Amma labari mara daɗi shine ɗaya daga cikin yan sandan, Edogi Bassey, ya rasa rayuwarsa, sannan kuma an rusa wani ɓangare na ginin wajen."
"Daga nan yan bindigan suka ƙara gaba zuwa ofishin dake Ika inda suka cigaba da mummunan aikinsu, amma an samu nasarar korarsu kuma babu wanda ya rasa rayuwarsa a ofishin."
Kakakin hukumar yan sandan ya ƙara da cewa ƙarin hare-haren da ake samu a kan jami'an yan sanda abun damuwa ne matuƙa, amma hukumomi na kokarin shawo kan lamarin.
Yace kwamishinan yan sandan jihar, Amiengheme Andrew, ya fara kai ziyara zuwa ofisoshin yan sandan jihar domin tabbatar da lafiyar jami'an yan sanda.
Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar dasu baiwa jami'an tsaro haɗin kai tare da basu bayanan da zasu taimaka musu wajen magance matsalar tsaro a jihar.
A wani labarin kuma Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara
Rundunar Sojin ƙasar nan ta bayyana matakin da zata ɗauka kan zargin da ake yiwa wani jami'inta na kisan wani mai siyar da kankana a jihar Zamfara.
Kakakin rundunar, Muhammed Yerima, yace tuni suka fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano gaskiyar abinda ya faru.
Asali: Legit.ng