Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed

Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed

- Ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammed yace bada jimawa ba yan Najeriya zasu ga sakamakon shirin da gwamnati keyi na kawo zaman lafiya a ƙasar nan

- Ministan yace magan-ganun da ake yaɗawa cewa gwamnati ta lulluɓe matsalar tsaron da ake fama da ita ba gaskiya bane

- Yace jami'an tsaro na sane da maɓoyar masu satar mutane, kawai suna bi a hankali ne dan kada su cutar da farar hula

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnati na ƙoƙarin kawo ƙarshen matalar tsaro a ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

Ministan yace zargin da wasu mutane suke cewa gwamnati bata damu da ta magance waɗannan matsalolin ba bashi da tushe balle makama.

Ya ƙara da cewa ba da jimawa ba yan Najeriya zasu ga sakamakon ƙoƙarin da gwamnati take na dawo da zaman lafiya a ƙasar nan, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed
Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ministan ya faɗi haka ne a wani jawabi da yayi a jihar Lagos, yace:

"Ba wani sabon labari bane cewa Najeriya na fama da matsaloli kala daban-daban na tsaro, na karanta wasu magan-ganu dake cewa gwamnati tana rufa-rufa kuma bata da dabarun yadda zata magance matsalolin."

"Ina mai tabbatar wa yan Najeriya cewa yayin da gwamnati ta fahimci ƙalubalen tsaron da ake fama dashi; ta'addanci, yan bindiga, satar mutane, da rikicin manoma da makiyaya, gwamnati ba ta lulluɓe komai."

KARANTA ANAN: Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa

"Kuma gwamnati ta tanadi duk abinda yakamata domin kawo ƙarshen matsalar kamar yadda zaku gani bada jimawa ba."

Muhammed ya ƙara da cewa gwamnati tasan maɓoyar masu satar mutane, ya ce hukumomin tsaro na bi a hankali ne saboda gudun haɗawa da fararen hula.

Yace: "Wuraren ɓoyon waɗannan masu satar mutanen ba abune boyayye a wajen jami'an tsaro ba, suna bi a hankali ne tare da kulawa domin gujewa cutar da mutanen da suka je kuɓutarwa."

"Jami'an tsaro suna da duk abinda ake buƙata domin magance ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama dashi."

A wani labarin kuma Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma zaɓaɓɓen sanata a jam'iyyar APC yace sama da kashi 75% na yan Najeriya basa jin daɗin wannan gwamnatin.

Sanata Rochas Okorocha na jihar Imo yace ya kamata gwamnatin tarayya ta canza salon da take amfani dashi wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel