Ba Zamu Bar Yan Adawa Suga Bayan Shugaba Buhari ba, Gwamnan APC

Ba Zamu Bar Yan Adawa Suga Bayan Shugaba Buhari ba, Gwamnan APC

- Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaƙ yace bai kamata gwamnonin APC su zura ido suna gani yan adawa na ƙoƙarin cutar da shugaba Buhari ba

- Gwamnan yace mafi yawancin gwamnonin da farin jinin shugaban suka samu damar ɗarewa mulki

- A cewarsa suna amfani da damar cewa Buhari bai cika yawan fitowa yana magana ba wajen ƙoƙarin kaishi ƙasa

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaƙ, yace mafi yawancin gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyyar APC "farin jinin Buhari yakai su kan madafun iko" kuma ba zasu bari yan adawa su wulaƙanta shi ba.

KARANTA ANAN: Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa

Gwamnan ya faɗi haka ne a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, yayin da yake raba tallafin azumi da akai wa take da "Baba nakowa" ga mabuƙata, naƙasassu da zawarawa a faɗin ƙananan hukumomin jihar 16.

Yace ya dace a girmama shugaba Buhari a matsayinsa na shugaba 'wanda ya maida hankali wajen jin dadin talakawa' kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Ba Zamu Bar Yan Adawa Suga Bayan Shugaba Buhari ba, Gwamnan APC
Ba Zamu Bar Yan Adawa Suga Bayan Shugaba Buhari ba, Gwamnan APC Hoto: @RealAARahman
Asali: Twitter

Gwamnan yace: "Mafi yawancin gwamnonin APC sun hau motar Buhari da farin jininsa ne yakaisu ga madafun iko."

KARANTA ANAN: Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC

"Duk da mungaji da irin jagorancin da ake mana anan Kwara a lokacin, amma shine ya jagoranci jam'iyyar mu zuwa ga nasara. Sabida haka ba zamu zauna muna kallo wasu suga bayan shugaban mu ba."

"Yayi abubuwan alkairi da yawan gaske amma saboda bai cika fitowa yana magana ba, shine wasu yan adawa suke amfani da wannan damar, suna kokarin ganin bayansa."

Gwamnan ya ƙara da cewa babu cikakken ɗan jam'iyyar APC ko masoyin Buhari da zai bari aga bayan shugaban.

A wani labarin kuma Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

Tsohon shugaban hukumar Inshoran lafiya NHIS, Usman Yusuf, yace yan bindiga na buƙatar tattaunawar zaman lafiya da malamai.

Yusuf yace ya fahimci haka ne a taron da ya halarta da yan bindiga kala-kala a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262