Wuf: Hotunan Matashi Bakar Fata da Budurwarsa Farar Fata Ya Jawo Cece-Kuce

Wuf: Hotunan Matashi Bakar Fata da Budurwarsa Farar Fata Ya Jawo Cece-Kuce

- Wani bakar fata ya sanya kafofin sada zumunta shewa yayin da ya bayyana rayuwar soyayyarsa

- Matashin ya watsa kyawawan hotuna yayin da yake nuna masoyiyarsa farar fata cikin zumudi

- Hotunan sun jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta ganin yadda masoyan ke nuna jin dadinsu

Da alama babu wani shamaki a abin da ake kira da soyayya ba ruwanta da ko kai wanene, ko da kuwa akwai banbancin launin fata. Wani bakin fata da masoyiyarsa farar fata sun kasance abin magana a kafofin sada zumunta.

Wannan ya biyo bayan da wani matashi, @ 1hekma_, ya watsa wasu hotuna a Twitter tare da nuna alfahari da nuna soyayyarsa mai sanyaya zuciya.

KU KARANTA: An Dakatar da Hakimin Kauyen da Ya Lakadawa Matarsa Duka Har Ta Mutu a Bauchi

Hotunan Matashi Bakar Fata da Budurwarsa Farar Fata Ya Jawo Cece-Kuce
Hotunan Matashi Bakar Fata da Budurwarsa Farar Fata Ya Jawo Cece-Kuce Hoto: @1hekma
Asali: Twitter

@ 1hekma_ wanda ya shahara a kafafen sada zumunta da kafofin watsa labaru na barkwanci ya watsa hoton kyakkyawar budurwa farar fata tare da shi. Ya kuma furta kaunarta a fili in da yake cewa:

"Ina matukar kaunarki.."

Ya zuwa lokacin yin wannan rahoton, tuni an riga an yi dangwale da suka haura 200,000 saboda tururuwan da masu amfani da Tuwita suka yi game da hotunansu.

Da yawa sun rasa ta cewa, kawai suna mamakin irin soyayyar masoyan ne. Wasu kuma sunyi musu fatan alkhairi a cikin zamantakewar su.

@tulsidas_khn ya rubuta:

"Wah! Ina muku murna da soyayya daga india saale madarchd."

@ Tsakee2 ya ce:

"Ko ya akayi muka kare a nan ma?"

@ Masedi94954412 gushe:

"Ooh wato har yanzu kuna tare. Har yanzu dai ina taya ku murna."

@_dwed_ ya ce:

"Bakar fata na farko kuma na karshe da (ya sami dangantaka) da 'yar Indiya."

KU KARANTA: Sheikh Mahi Ibrahim Inyass Ya Tabbatar da Nadin Sanusi II a Matsayin Khalifan Tijjaniyya

A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta nishadantar da 'yan kasa don saukaka mummunan yanayin da ‘yan Najeriya ke fuskanta na mawuyacin hali biyo bayan matsalar tsaro da ake ciki a kasar.

Wata mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, a ranar Litinin, 10 ga Mayu, ta shawarci ’yan kasar cewa duk da cewa kasar na cikin mawuyacin hali, amma tuni Shugaba Buhari ya fara gyara dimbin matsalolin ta hanyar ayyukan gina kasa.

Onochie, wacce ta tuno da cewa marigayi Chinua Achebe ya rubuta wani littafi a baya mai taken 'There was a Nation', ta lura cewa babu wani abu sabo da zai zo da sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.