Fadar Shugaban Kasa: Ku Nishadantu da Bidiyon Shugaba Buhari Na Rera Wakar Bob Maley
- Fadar shugaban kasa ta fidda wani bidiyo da ke nuna bidiyon shugaba Buhari na rera wakar Bob Marley
- Wata mai taimakawa shugaban kasa kan yada labarai ne ta fidda bidiyon a shafinta na Tuwita
- Ta bayyanawa 'yan Najeriya cewa, shugaba Buhari na kan aiki tukuru don dawo da martabar kasar
Fadar shugaban kasa ta nishadantar da 'yan kasa don saukaka mummunan yanayin da ‘yan Najeriya ke fuskanta na mawuyacin hali biyo bayan matsalar tsaro da ake ciki a kasar.
Wata mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, a ranar Litinin, 10 ga Mayu, ta shawarci ’yan kasar cewa duk da cewa kasar na cikin mawuyacin hali, amma tuni Shugaba Buhari ya fara gyara dimbin matsalolin ta hanyar ayyukan gina kasa.
KU KARANTA: Sheikh Mahi Ibrahim Inyass Ya Tabbatar da Nadin Sanusi II a Matsayin Khalifan Tijjaniyya
Onochie, wacce ta tuno da cewa marigayi Chinua Achebe ya rubuta wani littafi a baya mai taken 'There was a Nation', ta lura cewa babu wani abu sabo da zai zo da sauki.
Ta watsa wani faifan bidiyo mai dauke da hoton shugaban inda yake rera wata waka wacce shahararren mawakin nan na Reggae, Bob Marley ya yi.
@laurestar ta wallafa a shafinta na Tuwita cewa:
"There was a Nation" littafi ne da shahararren mawakin nan Chinua Achebe ya rubuta wanda ya mutu a 2013.
"Tare kuma da zuwan Mai Gyara, @ MBuhari, wanda ya fara gagarumin aiki na gina kasa daga tushe."
"Babu wani abu sabo da kalubale mai sauki ke kawo wa.
"Ku nishandantu da wannar wakar almara ta Bob Marley."
KU KARANTA: An Dakatar da Hakimin Kauyen da Ya Lakadawa Matarsa Duka Har Ta Mutu a Bauchi
A wani labarin, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta zargi Fadar Shugaban kasa da tsoratar da ’yan Najeriya da kalaman zagon kasa.
Da yake tsokaci game da kararrakin da aka nuna game da zargin yunkurin kifar da Shugaba Muhammadu Buhari, Daraktan Yada Labarai na kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya nemi gwamnati mai ci da ta magance matsalolin da kasar ke fuskanta.
NEF, a ranar Talata, ta shaida wa Daily Trust cewa babu wata fa’ida a fada wa ’yan Najeriya cewa wasu 'yan kasa da ba a ambata sunayensu ba suna shirya kifar da shugabanci ta hanyar da ba ta dace da demokradiyya ba a cikin kasar nan.
Asali: Legit.ng