Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

- Wani Jirgin kasa da ya taso daga Legas ya kauce daga kan hanyarsa a wani yankin jihar Kaduna

- An ruwaito cewa, babu asarar rai, kuma tuni hukumar kula da jiragen kasa ta fara aikin gyara

- Rahoton ya bayyana cewa, wasu bata-gari ne a suka lalata hanyar jirgin wanda ya jawo hatsarin

Wani jirgin kasa mai dauke da bututun ruwa daga jihar Legas zuwa Zariya a jihar Kaduna ya yi hatsari a wani yankin jihar ta Kaduna.

Hatsarin wanda ya afku a yankin Unguwar Kanawa da ke Kaduna ya tilasta wa jirgin tashi daga layin dogo, wanda hakan ya sa biyar daga cikin taragon jirgin kaucewa daga kan hanyar.

KU KARANTA: Likitan Da Ya Bayyana Maboyar Osama Bin Laden Na Neman Gwamnati ta Sake Shi

Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna
Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba a lamarin, injiniyan da ke kula da ayyukan Arewa na kamfanin jirgin kasa na Najeriya, Haruna Ahmed ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa hatsarin jirgin ya faru ne sakamakon lalata hanyoyin jirgin da wasu bata-gari suka yi.

Ya yi bayanin cewa, tuni Kamfanin Kula da Jiragen Kasa ya fara aikin kwashe sauran taragon da ba su fado daga kan hanya ba, yayin da ayyukan gyaran hanyoyin za su biyo baya nan gaba.

KU KARANTA: Wasu Kasurguman 'Yan Bindiga Sun Sheke Wani Kwamishanin Hukumar Fansho

A wani labarin, An tsinci gawar wani yaro da aka sace daga gidan iyayensa a wata unguwa da ke cikin garin Kaduna, kwanaki bakwai bayan an sace shi kuma aka ba da fansar Naira miliyan 5 don sakinsa.

Muhammad Kabir, da aka kashe, wanda aka dauke shi daga garin Badarawa da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, an yi imanin cewa masu garkuwar sun kashe shi.

An tsinci gawarsa a cikin magudanan ruwa a Kano bayan an kwashe mako guda ana bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.