Likitan Da Ya Bayyana Maboyar Osama Bin Laden Na Neman Gwamnati ta Sake Shi
- Likitan da ya taimakawa Amurka ta hallaka Osama ya nemi a sake bayan shekaru 10 a garkame
- CIA ta yi amfani da likitan dan kasar Pakistan ne musamman don bankado in da Osama bin Laden ke boye
- A baya an yankewa likitan hukuncin shekaru 23 a magarkama saboda bayyana Osama da ya yi
Yayin da ake cika shekaru 10 da kisan shugaban kungiyar Al-Qa'ida Osama bin Laden, likitan da ya taimaka wa hukumar leken asirin Amurka ta CIA bankado maboyar shugaban na Al Qa'ida ya yi kiran a sake shi.
Lauyan da ke kare likitan dan kasar Pakistan ya shaida wa BBC cewa ya kamata a sake shi.
An yanke wa Shakeel Afridi, hukuncin daurin shekaru 23 a gidan yari bayan kashe Osama a wani samamen da Amurka ta kai shekaru 10 da suka gabata.
KU KARANTA: An Tsinci Gawar Wani Yaron da Aka Sace a Magudanar Ruwa Bayan Biyan Fansa
Lauyan Afridi, Qamar Nadim Afridi, ya ce ya yi imanin cewa an yi yunkurin dakatar da soke hukuncin a shari’ar don kaucewa wanke likitan a cikin abin da ya bayyana a matsayin “karya”.
Wasu da dama sun yi imanin cewa an hukunta likitan ne saboda abin kunyar da ya janyo wa kasar Pakistan
Hukumar leken asirin ta CIA ta gudanar da aikin rigakafi ne na bogi shekaru 10 da suka shude a karkashin jagorancin Doctor Afridi, da nufin bankado maboyar Osama bin Laden.
KU KARANTA: Wasu Kasurguman 'Yan Bindiga Sun Sheke Wani Kwamishanin Hukumar Fansho
A wani labarin, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya ce mayakan Boko Haram sun yi kusa da babban birnin kasar., Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana lokacin da ya ziyarci sansanin 'Yan Gudun Hijira a ranar Litinin, gwamnan ya ce 'yan ta'addan sun karbe wani yanki na jihar bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza a kokarin samar da tsaro a jihar.
Ya ce ya tuntubi Gwamnatin Tarayya a lokuta daban-daban amma babu wani abu mai amfani da ya fito daga kokarinsa.
Bello ya yi gargadin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na kokarin mai da Kaure a karamar hukumar Shirroro da ke jihar ta zama hedikwatarsu kamar yadda suka yi a dajin Sambisa a jihar Borno.
Asali: Legit.ng