'Yan Najeriya da dama sun makale a yayin da dutse ke aman wuta a Tsibirin Caribbean
- Wasu 'yan Najeriya sun makale a tsibirin Caribbean sakamakon fashewar wani dutse mai aman wuta
- A halin yanzu an tattara wasu daga ciki zuwa wasu kasashen makwabta don gujewa shiga mayuwacin hali
- An nemitallafin Najeriya da sauran kasashen duniya duba da yadda mutane suka shiga halin ha'ula'i
'Yan Najeriya da dama na fargabar kasancewa cikin mawuyacin hali yayin da fashewar aman wuta daga wani dutse ya afkawa tsibirin Caribbean na St. Vincent da Grenadines wanda ke haifar da kaurar jama'a.
Akalla daliban Najeriya 230 ke karatun likitanci a tsibirin da kuma wasu masu yawon bude ido ke zaune a can.
Ya zuwa yanzu, Daily Trust ta tattara cewa an kwashe dubunnan mutane zuwa wurare masu aminci na tsibirin da kasashen makwabta ta hanyar amfani da bas da jiragen ruwa.
Karamin jakadan tsibirin a Najeriya, Dr Levi Odoe, ya nemi tallafi daga gwamnatin Najeriya da sauran masu fada a ji a duniya.
KU KARANTA: Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa
“Akwai 'yan Najeriya da yawa a tsibirin, kuma hakan na haifar da kalubale ga lafiya. Ana kwashe dangi zuwa wasu kasashe. Za mu yaba da taimako daga masu fatan alheri da abokan arziki,” in ji Dokta Odoe.
'Yan kasar da ke cikin matsanancin hali sun watsa faifan bidiyo game da fashewar, wanda ya fara a ranar 9 ga Afrilu lokacin da bakin toka da hayaki ya turnuke sararin samaniya a kusan nisan kilomita 6.
Wani mai amfani da shafin Twitter, Rahym R. Augustin-Joseph ya wallafa a shafinsa na Twitter, @RahymRJoseph: "Mu tuna da sanya mutanen St. Vincent da Grenadines cikin addu'o'inmu a irin wannan lokacin da ake cikin na mawuyacin hali."
St. Vincent da Grenadines suna da dutse mai aman wuta a tsaunin La Soufrière, wanda ya kai kololuwar mita 1,234.
Wannan shi ne karo na hudu da aman wutar dutsen ya afku a tsibirin bayan na farko da aka yi a shekarar 1718. Fashewa ta shekarar 1902 ta haifar da mutuwar mutane sama da 1000, yayin da fashewar 1979 ta lalata kadarorin da suka kai $ 100m.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Likitocin Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga
A wani laarin, Wasu fitattun ‘yan Najeriya sun hallara a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja domin kaddamar da wani littafi da aka rubuta domin girmama uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a ranar Alhamis.
Kaddamar da littafin tarihin rayuwar mai taken, ‘Aisha Buhari: Being different’, ya samu halartar mutane duk da cewa wasu daga cikin manyan mutanen da aka gayyata ba su halarci taron ba, Daily Trust ta ruwaito.
Babban mataimakiya na musamman ga shugaban kasa kan harkokin mulki da harkokin mata, Dr Hajo Sani ce ta rubuta littafin.
Asali: Legit.ng