Dangote, wasu fitattu sun ba da makudan miliyoyi a bikin littafin Aisha Buhari

Dangote, wasu fitattu sun ba da makudan miliyoyi a bikin littafin Aisha Buhari

- A yau aka kaddamar da littafin da aka rubuta na tarihin matar shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Wasu fitattun 'yan Najeriya sun hallara, inda suka zuba makudan kudade a sayen kofin littafin

- Duk da cewa, wasu manyan basu hallara ba, amma sun turo sako mai tsoka a bikin na kaddamarwa

Wasu fitattun ‘yan Najeriya sun hallara a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja domin kaddamar da wani littafi da aka rubuta domin girmama uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a ranar Alhamis.

Kaddamar da littafin tarihin rayuwar mai taken, ‘Aisha Buhari: Being different’, ya samu halartar mutane duk da cewa wasu daga cikin manyan mutanen da aka gayyata ba su halarci taron ba, Daily Trust ta ruwaito.

Babban mataimakiya na musamman ga shugaban kasa kan harkokin mulki da harkokin mata, Dr Hajo Sani ce ta rubuta littafin.

KU KARANTA: El-Rufai: 'Yan bindiga sun rasa 'yancin rayuwa, dole ne a shafe a doron kasa

Dangote, wasu fitattu sun ba da makudan miliyoyi a bikin littifin Aisha Buhari
Dangote, wasu fitattu sun ba da makudan miliyoyi a bikin littifin Aisha Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdulsamad Rabiu, Muhammadu Indimi, da Jim Ovia na daga cikin wadanda suka tura wakilai.

Amma Asiwaju Bola Tinubu, Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa da gwamnoni da yawa sun hallara.

A taron akwai jerin wadanda suka sayi kofi na littafin da abin da suka bayar.

1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (N20m),

2. Alhaji Aliko Dangote (N30m),

3. Alhaji Abdulsamad Rabiu (N25m),

4. Misis Folorunso Alakija (N10m),

5. Cif Kessington Adebutu (N10m).

Shugaban NGF kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi alkawarin tura wasu kudade da ba a bayyana yawansu ba don sayen nasu a madadin gwamnoni da sanatoci.

Sanata Daisy Danjuma da wasu ma sun bi sahun masu rike da mukaman siyasa.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun saki mambobin Cocin RCCG 8 da suka sace a Kaduna

A wani labarin, ‘Yan Najeriya da-dama da ke amfani da kafafen yada labarai da sada zumunta sun yi magana game da littafin Aisha Buhari da aka kaddamar.

A yau ne Hajo Sani ta kaddamar da littafin da ta rubutu a kan rayuwar uwar gidanta, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, inda aka yi biki a Aso Villa.

Dinbin ‘yan siyasa da attajirai da manyan kasa sun samu halartar bikin kaddamar da wannan littafi mai suna “Aisha Buhari, ta fita dabam” dazu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel