Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa

Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Dangote murnanr cika shekaru 64 a duniya

- Shugaban ya siffanta Dangote da mutumin kirki mai tallafawa 'yan Najeriya da Afrika

- Ya kuma bayyana cewa, al'umomi masu zuwa nan gaba ba za su taba mantawa da shi ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote murnar karin shekara guda a shekarunsa, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ya mika sakonsa na fatan alheri ga daya daga cikin manyan masu hannu da shunin na Afirka a cikin wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu.

Shugaban ya bayyana Dangote, wanda ya cika shekaru 64 a ranar Asabar, a matsayin babban abokin tarayya kuma "Jarumin yakin Korona" wanda ya ci gaba da nuna cikakken imani da kasar.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Likitocin Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga

Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa
Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa Hoto: nairaland.com
Asali: UGC

Ya lura cewa duk da cewa annobar Korona ta sanya babbar damuwa ga kasashe da yawa, an dan rage matsalar ga ‘yan Najeriya da gwamnati.

Shugaba Buhari ya danganta hakan da goyon baya da hadin kan 'yan kasa kamar Dangote wanda ya ce suna matukar nuna jin kai da sadaukarwa ga dan adam ta hanyoyin su.

Ya kuma yaba mishi saboda bude fuka-fukansa da yake da burin karfafa matasa da kwararru da dama a Najeriya da ma sauran nahiyoyi ya kuma bukace shi da ya ci gaba da yin hakan.

Shugaban ya yi imanin wadannan kokari na Dangote za su shiga cikin tarihi kuma al'ummomi masu zuwa za su tuna da shi.

Ya yi wa Dangote fatan karin shekaru masu yawa na rayuwa cikin koshin lafiya da yi wa kasarsa hidima da kuma bil'adama baki daya.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Rikici ya barke a gidan yarin Bauchi, mutum 7 sun jikkata

A wani labarin daban, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana kaunar mutanen Ogbia, wata karamar kabilar Ijaw a cikin jihar Bayelsa.

Ministan ya ce dalili kuwa daya ne, saboda dansu, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya bar masa mulki cikin lumana a 2015, The Nation ta ruwaito.

Sylva ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya ke duba aikin da ake yi na samar da Man Fetur da Gas na Kasa (NOGaPS) wanda Hukumar NCDMB ke ginawa a Emeyal 1, karamar hukumar Ogbia ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel