Da dumi-dumi: Likitocin Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga

Da dumi-dumi: Likitocin Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga

- Kungiyar likitocin Najeriya ta janye yajin aikin da ta fada a makon da ya gabata; 1 ga Afrilu

- Kungiyar likitocin ta bayyana haka ne a daren Asabar bayan wata tattaunawa da gwamnati

- Sai dai, kungiyar ta ce, yajin aikin ta dage shi zuwa makwanni hudu masu zuwa a gwamnati ta dubesu

Kungiyar Likitocin Kasa (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 1 ga Afrilu, 2021.

Shugaban NARD din, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, ya fadawa jaridar The Nation dakatarwar ta dogara ne da wasu kyawawan sakamako daga tattaunawar da aka yi da gwamnati.

Duk da haka ya ba gwamnati wa'adin makonni hudu don biyan bukatunsu da suka koka akai.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Rikici ya barke a gidan yarin Bauchi, mutum 7 sun jikkata

Da dumi-dumi: Likitocin Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga
Da dumi-dumi: Likitocin Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce: “An dakatar da yajin aikin. Gwamnati ta ba mu kyakkyawan sakamako daga tattaunawarmu.

"Mun yi taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) awa daya da ta gabata, kuma mun yanke shawarar dakatar da yajin aikin na tsawon makonni hudu."

KU KARANTA: Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa

A wani labarin daban, Alkalumman da hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ke fitarwa game da cutar korona a kasar ya nuna cewa tsawon mako daya kenan cutar ba ta yi kisa ba a fadin kasar, BBC ta rahoto.

Alkalumman wadanda cutar ta kashe ba su sauya ba tun daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 7 ga watan Afrilu inda cutar ta kashe jimillar mutum 2,058 tun shigowarta.

Alkalumman da hukumar ta fitar ranar Talata sun nuna cewa karin mutum 58 da sun kamu da cutar korona a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.