Kotu ta sanar da ranar da zata yanke hukunci kan hallacin tsawaita wa'adin IGP Adamu

Kotu ta sanar da ranar da zata yanke hukunci kan hallacin tsawaita wa'adin IGP Adamu

- Wata babbar kotu dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta bayyana ranar da zata yanke ma IGP hukunci

- An dai shigar da ƙarar IGP Muhammed Adamu gaban kotun ne kan ƙarin wa'adin da shugaba Buhari ya masa

- Lauyan da ya shigar da ƙarar yace IGP bai da hurumin cigaba da zama akan kujerar sa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja, ta tsaida ranar 16 ga watan Afrilu a matsayin ranar da zata yanke hukunci kan karar da ke neman a cire Mohammed Adamu a matsayin shugaban yan sandan Najeriya.

Adamu wanda aka nada a 2019, ya cika shekaru 35 na aiki ranar 1 ga watan Fabrairu,, kuma an tsammanin shugaban kasa ya maye gurbinsa da wani.

KARANTA ANAN: Tafiyar Landan: Ka mikawa Osinbajo mulki, kayi zamanka a can kada ka dawo: Wasu yan Najeriya ga Buhari

Saidai kuma a 4 ga watan Fabrairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara masa wa'adin watanni uku, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wani lauya, Maxwell Opara, ya maka shugaban yan sandan a kotu inda ya kafa hujja da sashi na 215 na kundin tsarin mulkin Najeriya da sashi na 7 na kundin yan sanda na 2020.

Kotu ta Sanar da ranar da zata yanke ma Sufetan yan sanda na ƙasa Hukunci
Kotu ta Sanar da ranar da zata yanke ma Sufetan yan sanda na ƙasa Hukunci Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A cewar lauyan, Adamu ba zai cigaba da rike mukaminsa ba saboda ya riga da ya yi ritaya daga hukumar yan sanda.

KARANTA ANAN: Gemu ba ya hana ilimi: 'Yar shekara 62 ta shiga makarantar firamare don neman ilimi

Da yake kare kansa, IGP ya fadi ma kotu cewa sabon kundin tsarin aikin yan sanda ya bashi hurumin shekara 4 kan kujerar sa wanda zai kare kodai a 2023 ko 2024.

Da suke nuna goyon bayansu kan matsayin da Adamu ya dauka, shugaba Muhammadu Buhari da Abubakar Malami ta hannun lauyansu sun fadi ma kotun cewa sabuwar dokar ta bashi hurumin cigaba da zama kan kujararsa har zuwa 2023 ko 2024.

Bayan jin ta bakin dukkanin bangarorin biyu, Alkalin kotun Ahmed Muhammad ya tsayar da ranar 16 ga watan Afrilu domin yanke hukunci.

A wani labarin kuma Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ta sanar da cewa ana amfani da kudin fansa ne wurin assasa Boko Haram

Bayan zantawarsu da shugaban kasa, Fayemi ya sanar da cewa wasu wadanda suke daukar nauyin ta'addanci ne ke yin na Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel