Tafiyar Landan: Ka mikawa Osinbajo mulki, kayi zamanka a can kada ka dawo: Wasu yan Najeriya ga Buhari

Tafiyar Landan: Ka mikawa Osinbajo mulki, kayi zamanka a can kada ka dawo: Wasu yan Najeriya ga Buhari

- Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa kamar yadda ya saba

- Fadar shugaban kasa ta ce zai kwashe kimanin makonni biyu a Birtaniya

- Buhari ya gana da hafsoshin tsaro yayinda yake shirin wannan tafiya

Wasu yan Najeriya sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya mika ragamar mulki hannun mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbanjo kafi ya tafi duba lafiyarsa birnin Landan.

A yau Talata Shugaba Buhari zai tafi kasar Birtaniya duba lafiyarsa, a cewar fadar shugaban kasa.

Amma fadar shugaban kasan ba tayi magana kan mikawa mataimakin Buhari, Osinbajo, mulki ba kamar da kundin tsarin mulki ya tanada.

Buhari zai kwashe makonni biyu tare da wasu hadimansa a Landan.

Wasu yan Najeriya a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan tafiyar shugaban kasa.

Wasu sun ce shin me yasa shugaban kasa bai sanar da mika mulki ga mataimakinsa ba ko kuma yana tsoron wani abu ne.

Wasu kuma sun ce kawai ya mikawa mataimakinsa mulki kuma yayi zamansa a Landan kada ya dawo.

KU DUBA: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane

Tafiyar Landan: Ka mikawa Osinbajo mulki, kayi zamanka a can kada ka dawo: Wasu yan Najeriya ga Buhari
Tafiyar Landan: Ka mikawa Osinbajo mulki, kayi zamanka a can kada ka dawo: Wasu yan Najeriya ga Buhari Credit: Presidency
Source: Facebook

DUBA NAN: Shugaban Majalisa ya roki Shugaba Buhari ya jarraba shawarwarin da Tinubu ya bada

@Cisser_maye: "In yaje karya dawo... Da shi da ba shi duk daya wlh..."

@NosaAguebor yace, "Ina tambaya - shin ya mika ragamar mulki ga wanda zai mulki kasar a bayansa ko kuma ya cigaba da jagorantar kasar daga can?

@von_Bismark, “Ba shi da amfani a nan. Yayi zamansa a can sai ya shirya dawowa. ko a jikinmu."

@Boxypiper, "Shugaba Buhari ya aikewa majalisar dokoki sako kuma ya mikawa VP mulki a bayansa."

Shehu S Habibillah: "Bamu amfanada kai komai ba amulkinka sai talauci da tsadar rayuwa kaje Allah ya saka mana"

Muhammad Dalati: "Allah shi kara lafiya Baba. Talakawanka suma, suna da bukatar a duba lafiyarsu. Baza dai a kaisu London ba, amma a gyara tsarin kiwon lafiya na kasa."

Idan Allah ya dawo da kai lafiya, don Allah ka kai ziyarar bazata a asibitocin karkara zaka gane abinda nake nufi."

Bilyaminu Hamme Reme: "Baba zan baka shawara idan kaje kayi Kamar wata 9 Shan kafin kadawo jikin naka zai Kara warwarewa."

Source: Legit

Tags:
Online view pixel