Gemu ba ya hana ilimi: 'Yar shekara 62 ta shiga makarantar firamare don neman ilimi

Gemu ba ya hana ilimi: 'Yar shekara 62 ta shiga makarantar firamare don neman ilimi

- Wata dattijuwa 'yar shekara 62 ta burge kanta da shiga makarantar firmare duk da tsufanta

- Ta bayyana cewa, tana da burin bada gudunmawa ga al'umma, shi yasa ta koma makaranta

- Ta kuma bayyana cewa, da zarar ta kammala karatunta, za ta lallaba ta nemi kujerar majalisa

A shekara 62, yawancin talakawa mantawa suke da batun makaranta gaba daya su dukufa su mai da hankali kan tsufa da more rayuwa tare da jikokinsu.

Ga Maureen Ngoma ta kasar Zambiya kuwa, labarin ya sha ban-ban, domin tsufa ya zama farkon sabon salo a gare ta a fannin ilimi.

Dattijuwar mai yara tara kwanan nan ta shiga makarantar firamare ta Senga Lumbwe a Lusaka karkashin shirin yaki da jahilci a matsayin dalibar aji na 8.

Ta ce: "Ina so in yi aiki a babban ofishi kuma in ba da gudunmawata ga al'umma idan na gama makaranta."

KU KARANTA: Korona ta kusa fita daga Najeriya, yawan masu kamuwa da ita ya ragu

Gemu ba ya hana ilimi: 'Yar shekara 62 ta shiga makarantar firamare don neman ilimi
Gemu ba ya hana ilimi: 'Yar shekara 62 ta shiga makarantar firamare don neman ilimi Hoto: Timesofzambianewspaper
Asali: Facebook

Jaridar Times of Zambia ta rawaito cewa Maureen na da burin shiga aikin soji a Zambiya ko kuma shiga harkar siyasa, kuma za ta nemi kujerar Majalisar Dokokin Lusaka ta Tsakiya da zarar ta kammala karatunta.

A cewar dattijuwar, mata masu zaman kansu da ke aiki a ofisoshi masu mutunci suna ba ta kwarin gwiwa.

Cewa tana da karancin ilimin boko da shi ke ci mata tuwo a gwarya na zama kamar su, shine dalilin da yasa ta yanke shawarar daura damarar komawa makaranta don neman ilimi.

Labarin karatun Maureen ya tsaya shekaru 45 da suka gabata lokacin da ta yi watsi da makaranta tana da shekaru 17 tayi aure.

A wani hoto da aka yada a yanar gizo, an ga Maureen tare da jikokinta wadanda ke mata rakiya zuwa makaranta.

KU KARANTA: Malaye: Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo kan tafiya Landan

A wani labarin,Wani tsohon malamin jami'a mai ritaya dan shekaru 80, Farfesa Muritala Haroon, a ranar Alhamis ya fada wa Kotun Al’adu da ke zaune a Mapo, cewa matarsa, Afsat, har yanzu ta ki amincewa da shi, Daily Nigerian ta ruwaito.

A lokacin da aka ci gaba da sauraran karar, Mista Haroon ya ce: “Matata ba ta bi shawarar da wannan kotu ta ba ta ba don samar da damar zaman lafiya ya ci gaba ta hanyar amincewa da aiwatar da aikinta na matar aure.

Sai dai, Afsat ba ta halarci zaman kotun ba lokacin da aka kira ta kuma babu wanda ya wakilce ta a kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel