Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni

Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni

- Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ta sanar da cewa ana amfani da kudin fansa ne wurin assasa Boko Haram

- Bayan zantawarsu da shugaban kasa, Fayemi ya sanar da cewa wasu wadanda suke daukar nauyin ta'addanci ne ke yin na Boko Haram

- Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce koda aka sauya shugabannin tsaro, basu tsammanin sauyi da gaggawa

Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), a jiya ta bayyana cewa ana amfani da kudin fansa wurin asassa wutar ta'addancin Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, shugaban NGF kuma Gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya sanar da hakan a yayin taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.

A yayin amsa tambayoyi daga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron, shugaban NGF ta ce: "Akwai alaka tsakanin Boko Haram da 'yan bindigan dake yankin arewa maso yamma. Wasu daga cikin masu daukar dawainiyar Boko Haram sune ke da 'yan bindiga.

KU KARANTA: Ganduje ya karfafa yaki da rashawa a jihar Kano, Cewar Tinubu

Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni
Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rundunar sojin hadin guiwa ta MNJTF za su iya kawo karshen Boko Haram, Idris Deby

"Suna amfani da kudin da suka samu daga fansa domin aiwatar da hare-haren yankin arewa maso gabas.

"Don haka ya dace mu duba yanayin abubuwa da kuma yadda zamu shawo kansu. Dole ne mu hada kai tare da shawo kan matsalar."

Ya jinjinawa kokarin hukumomin tsaro na kasar nan inda yace duk da yana daga cikin masu assasa cewa a sauya shugabannin tsaro, baya tsammanin ganin sauyi da gaggawa.

Gwamna Fayemi yace, "Da farko dai shugaban kasa ya dauka turba mai kyau wurin sauya shugabannin tsaro. Zan iya tunawa cewa ni nake ta maganganu a madadin takwarorina.

"Ba mu taba cewa ga wadanda zai nada ba ko a lokacin da muka bukaci sauyin da zai kawo cigaba, amma kuma bama tsammanin da gaggawa za mu ga sauyin."

A wani labari na daban, zababben shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya jaddada mayar da hankalinsa wurin kakkabe dukkan rashawa a kasar nan inda yace doka da tsoron Allah ne jagororinsa.

Ya bayyana rashawa a matsayin mummunan lamarin dake hana cigaban kasar nan inda yace akwai bukatar a hada karfi da karfe wurin ganin bayanta a kasar nan.

Channels TV ta wallafa cewa, Bawa ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a, 26 ga watan Maris 2021 a wata tattaunawa ta musamman da aka yi dashi a gidan talabijin na kasa na NTA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel