Matsalar Tsaro: Ni ba wakilin tattaunawa da 'yan bindiga bane, Inji Sheikh Gumi

Matsalar Tsaro: Ni ba wakilin tattaunawa da 'yan bindiga bane, Inji Sheikh Gumi

- Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa shifa ba wakilin tattaunawa da 'yan bindiga bane

- Shahararren malamin ya faɗi haka ne ya yin da tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya kai masa ziyara

- Sani ya kai ma malamin ziyara ne kan ɗaliban da aka sace a makaranta FCFM dake Kaduna da kuma mambobin RCCG takwas da aka sace kwanan nan.

Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya ce shi fa ba aikin sa bane tattaunawa da yan bindiga.

Rahoton jaridar Dailytrust ya nuna cewa malamin ya faɗi haka ne ya yin da tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya kai masa ziyara.

KARANTA ANAN: Malaye: Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo kan tafiya Landan

Shehu Sani ya kaima malamin ziyara ne kan ɗalibai 39 da aka sace a makarantar koyon zamanantar da gandun daji FCFM dake Afaka, jihar Kaduna.

Da kuma mambobin ƙungiyar addinin kirista (RCCG) takwas da aka sace kwanan nan.

Gumi yace duk wasu shirye-shirye da yakamata ayi anyi don ganin an kuɓutar da ɗaliban waɗanda suka ɗauki tsawon makwanni biyu a hannun yan bindigan.

Ya ce akan lamarin ɗaliban mun yi duk abinda yakamata, har taro muka yi da iyayen ɗaliban kan suje su zauna da gwamnati.

Matsalar Tsaro: Ni ba wakilin tattaunawa da 'yan bindiga bane, Inji Sheikh Gumi
Matsalar Tsaro: Ni ba wakilin tattaunawa da 'yan bindiga bane, Inji Sheikh Gumi Hoto: @Ahmad_Gumi
Source: Twitter

A cewar sheikh Gumi:

"Na faɗawa iyayen ɗaliban inda matsalar take, sunje sun zauna da gwamnati sannan suka dawo wurina. Ni ba wakilin tattaunawa da yan bindiga bane."

"A duk tattaunawar da muka yi a baya muna tabbatar da akwai wakilan gwamnati tare da mu, kafin gwamnati ta bada umarnin harbe duk wanda aka gani ɗauke da bindiga."

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ya ba mutane 5 mukamai kafin ya bar Najeriya, ya tafi ganin Likita a Ingila

Amma a kan ɗaliban kwalejin, muna iya bakin ƙoƙarin mu ta hanyar tuntuɓa muga ta yadda za'a warware matsalar.

Satin da ya gabata sheikh Gumi ya shaidawa jaridar Dailytrust cewa umarnin harbi da gwamnati ta bayar ya dakatar da ƙoƙarinsa na kuɓutar da mutanen da aka sace.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba jami'an tsaro umarnin harbi ga duk wanda suka gani ɗauke da makami ba bisa ƙa'ida ba a cikin Daji.

Waɗanda suka sace ɗalibai 39 a Kaduna sun nemi a biyasu 500 miliyan amma gwamnatin Kaduna ta sha alwashin bazata zauna da yan bindiga ba.

A wani labarin kuma Gwamnonin Arewa sun taya Bola Tinubu murnanr cika shekara 69

Kungiyar gwamnonin Arewa ta taya Bola Ahmad Tinubu murnar cika shekaru 69 a duniya.

Kungiyar ta kuma yabawa Tinubu da irin jajircewar da yake yi wajen wanzar da zaman lafiya.

Source: Legit.ng

Online view pixel