Malaye: Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo kan tafiya Landan

Malaye: Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo kan tafiya Landan

- Dino Malaye ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mulki ga mataimakinsa

- Malaye ya bayyana hakan ne a cewarsa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada

- Ya kuma roki shugaban da ya aikata hakan kafin ya bar kasar a rubuce zuwa ga majalisar dokoki

Tsohon Sanata, Dino Melaye ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga Mataimakinsa, Yemi Osinbajo yayin da yake shrin tafiya zuwa Landan don duba lafiyarsa, PM News ta ruwaito.

Fadar Shugaban kasa ta sanar a ranar Litinin cewa Buhari zai yi tafiya zuwa Landan ta kasar Ingila don duba lafiyarsa kuma zai dawo nan da makonni biyu.

KU KARANTA: Idan Najeriya ta tarwatse, dole kuyi Visa domin shiga Kano, in ji Osinbajo ga 'yan kudu

Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo, in ji Dino Malaye
Ya kamata Buhari ya mika mulki dungurugum ga Osinbajo, in ji Dino Malaye Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Don haka Dino Melaye, a cikin wani sakon Twitter ya ce ya kamata Buhari ya mika mulki ga Mataimakin Shugaban kasa ta hanyar rubuta wasika zuwa ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Ya bukaci cewa shugaban ya yi hakan kafin barin kasar a ranar Talata.

Ya rubuta: "Yakamata shugaban kasa ya mika mulki ga Mataimakin Shugaban kasa ta hanyar rubuta wasika zuwa ga Majalisar Kasa kafin ya bar kasar kamar yadda tsarin mulki ya tanada."

KU KARANTA: Marwa da wasu jami'an NDLEA sunyi gwajin ba-zata na shan miyagun kwayoyi

A wani labarin daban, A cewar Adesina, Buhari za kwashe fiye da mako guda a Landan kuma zai dawo cikin mako na biyu a watan Afrilu.

"Shugaba Buhari zai garzaya Landan, Birtaniya, ranar Talata 30 ga Maris, 2021 domin duba lafiyarsa," Adesina yace.

"Shugaban zai gana da hafsoshin tsaro da safe, sannan ya tafi. Ana kyautata zaton zai dawo cikin mako na biyu a Afrilu, 2021."

Asali: Legit.ng

Online view pixel