Shugaba Buhari ya ba mutane 5 mukamai kafin ya bar Najeriya, ya tafi ganin Likita a Ingila

Shugaba Buhari ya ba mutane 5 mukamai kafin ya bar Najeriya, ya tafi ganin Likita a Ingila

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin Darektocin NASENI

- Sanarwar nadin mukamin ya fito ne kafin aji labarin zai bar Najeriya a dazu

- Olayinka Adunni Komolafe ce ta zama sabuwar Darektar hukumar NASENI

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabanni a hukumar NASENI mai kula da kirkiren kimiyya da fasaha a Najeriya.

Shugaban kasar ya yi wannan sauya-sauye ne a yunkurin gwamnatin tarayya na ganin an gyara wannan ma’aikata domin ta yi aiki da kyau.

Nadin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya fito ne ta ofishin babban ma’aikacin fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim A. Gambari.

KU KARANTA: Hazo ya hana jiragen sama tashi su halarci bikin maulidin Bola Tinubu

Daily Trust ta ce an sa hannu a wasikar Ibrahim A. Gambari ne a ranar 24 ga watan Maris, 2021.

Jaridar ta ce fadar shugaban kasa ta sanar da shugaban ma’aikatar NASENI game da wannan nadin mukamai da mai girma shugaban kasa ya yi.

Kamar yadda ma’aikatar ta NASENI ta bayyana a wani jawabi da ta fitar a ranar Litinin, wasikar shugaban kasar ta samu shigo wa hannunta.

Mai magana da yawun bakin NASENI, Olusegun Ayeoyenikan ya bayyana haka a wata sanarwa.

KU KARANTA: Saudiyya ta gindaya sharuda ga masu yin aikin Umrah a 2021

Shugaba Buhari ya ba mutane 5 mukamai kafin ya bar Najeriya, ya tafi ganin Likita a Ingila
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: APC

Wadanda aka nada su ne: Dr. (Mrs.) Olayinka Adunni Komolafe, sakatafiyar ma’aikatar, sai Injiniya Farfesa Danshehu Bagudu Gwandangaji.

Sai kuma Farfesa Umar Ibrahim Gaya, Misis Nonyem Onyechi, da Mista Ibrahim Baba Dauda.

Darektcoin za su kula da harkar fasahan, gudanar wa, tsare-tsare, cigaban kasuwanci, da harkar kudi. Za su yi shekara biyar a wannan kujeru.

Dazu nan mu ka ji cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sake zuwa birnin Landan, domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya bayyana cewa Buhari zai tafi gobe Talata, 30 ga watan Maris, ana sa ran ya dawo a cikin watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel