"Ku Ce Ni da Kwankwaso Mun Gaza"; Peter Obi Ya Dauki Muhimmin Alkawari ga 'Yan Najeriya

"Ku Ce Ni da Kwankwaso Mun Gaza"; Peter Obi Ya Dauki Muhimmin Alkawari ga 'Yan Najeriya

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalar raba mutane da muhallansu saboda rikice-rikice
  • Obi ya yi alkawarin haɗa kan ’yan Najeriya da tabbatar da tsaron rayukansu, musamman a jihohin Plateau da Benue
  • Ya ce zai ɗauki gwamnatinsa a matsayin wadda ta gaza idan wani ɗan Najeriya yana sansanin ’yan gudun hijira bayan watanni 18

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin magance matsalar ’yan Najeriya da rikice-rikicen tsaro suka tilasta barin gidajensu.

Obi ya bayyana cewa gwamnatinsa ta zama wadda ta gaza idan har wani ɗan Najeriya yana zaune a sansanin ’yan gudun hijira (IDP) bayan watanni 18 da kama aikinsa.

Obi ya dauki alkawari ga 'yan Najeriya
Peter Obi na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya yi wannan alƙawarin ne ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 a Jos, babban birnin Jihar Plateau, yayin da yake bayyana shirye-shiryensa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

Ya ce zai bai wa haɗin kan ƙasa da tsaro muhimmanci, yana mai cewa rarrabuwar kan ’yan Najeriya bisa ƙabila da addini na ƙara kawo cikas ga ci gaban ƙasar.

A cewarsa, ya zama wajibi ’yan Najeriya su fahimci cewa duk da bambancin ƙabila da addini, al’umma ɗaya ce kuma ya kamata su kasance da haɗin kai.

Ya yi magana kan kashe-kashe a Plateau da Benue

Obi ya ce babban abin da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai shi ne haɗa kan ƙasar da kuma tabbatar da cewa kowa yana rayuwa cikin aminci.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da kashe mutane a wasu yankuna, musamman a jihohin Plateau da Benue, inda hare-hare suka tilasta wa jama'a barin gidajensu.

"Alƙawarinmu shi ne haɗa kan Najeriya, domin a yau babu haɗin kai. Mun rarrabu bisa ƙabila da addini, alhali bai kamata hakan ya kasance ba, domin mu ’yan Najeriya ne.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Tinubu ya sake daukarwa 'yan Najeriya alkawarin da ya gaza cikawa

“Abu na biyu shi ne tabbatar da tsaron ƙasar. Babban abin da muka sa a gaba shi ne ganin ’yan Najeriya suna rayuwa cikin aminci.
“A wurare kamar Plateau da Benue, inda ake kashe mutane kullum, ina tabbatar muku cewa babu wata uwa da za ta sake yin kuka saboda rasa ’ya’yanta. Babu macen da za ta sake fuskantar radadin rasa mijinta, haka kuma babu uba da zai rasa matarsa.” In ji shi.

Ya ambaci ziyarar da ya kai yankunan Plateau

Obi ya jaddada cewa ba zai amince da ci gaba da zaman ’yan Najeriya a sansanonin gudun hijira na tsawon lokaci ba bayan hawansa mulki.

“Na faɗa a baya, kuma zan sake faɗa cewa bayan shekara ɗaya zuwa watanni 18 da fara aiki, idan har wani ɗan Najeriya yana cikin sansanin ’yan gudun hijira, to mun gaza.” In ji shi.

Ya kuma bayyana cewa yana da masaniya kan matsalolin tsaro da al'ummomin Plateau ke fuskanta, sakamakon ziyarar da ya kai wasu yankunan da hare-hare suka shafa.

Obi ya ambaci Bokkos, Mangu da Barkin Ladi a matsayin wuraren da ya ziyarta domin sanin halin da mazauna yankunan ke ciki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bayyana abin da Tinubu yake tsoro kan zaben 2027

“Babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya je Bokkos, Mangu da Barkin Ladi, saboda haka na san irin radadin da mutane ke ciki.” In ji shi.

Me Obi ya ce kan haɗin gwiwarsa da Kwankwaso?

Tsohon gwamnan ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa haɗin gwiwarsa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda zai zama mataimakinsa idan aka zaɓe su, zai taimaka wajen magance matsalar garkuwa da mutane da rashin tsaro.

“Ina tabbatar muku cewa idan ni da Kwankwaso muka zama shugaban ƙasa da mataimakinsa, babu wanda zai yi garkuwa da yaran makaranta ya tafi da su cikin daji.” In ji shi.

Peter Obi ya sha alwashi kan zaben 2027
Peter Obi na jawabi a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Wike ya ragargaji Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya ragargaji ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, kan rashin ƙwarewa da dabarun gudanar da mulkin ƙasa.

Ministan ya ce Peter Obi ba shi da ƙarfin gwiwar fuskantar tarin ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, inda ya ƙara da cewa zai gudu ne kawai zuwa ƙasar Kamaru idan har aka ɗaura masa nauyin shugabancin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng