Gwamnonin Arewa sun taya Bola Tinubu murnar cika shekara 69
- Kungiyar gwamnonin Arewa ta taya Bola Ahmad Tinubu murnar cika shekaru 69 a duniya
- Kungiyar ta kuma yabawa Tinubu da irin jajircewar da yake yi wajen wanzar da zaman lafiya
- Hakazalika kungiyar ta siffanta shi da matsayin wani babban jigo a siyasar Najeriya baki daya
Kungiyar Gwamnonin Arewa sun taya Shugaban Jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu murnar cika shekaru 69 a duniya, jaridar Vangaurd ta ruwaito.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan Filato, Simon Lalong, ya taya shugaban murna ne a cikin sakon taya murna da Daraktansa na yada Labarai da Harkokin Jama'a, Dakta Makut Macham, ya gabatar a ranar Litinin a Jos.
Lalong ya bayyana shugaban na APC a matsayin fitaccen dan siyasa kuma gogagge a fannin mulki, wanda ya yi fice a ci gaba na fagen zamantakewar siyasa da zamantakewar al'umma.
KU KARANTA: Idan Najeriya ta tarwatse, dole kuyi Visa domin shiga Kano, in ji Osinbajo ga 'yan kudu
Ya ce, Tinubu ya tsaya tsayin daka a matsayin dan siyasa, mai kishin kasa, kuma mai kishin al'umma, wanda ke nuna hangen nesa, sassauci, da rashin nuna bambanci a yayin gina kasa da tattaunawar kasa.
Lalong ya kuma bayyana shi a matsayin jigo, wanda ke ci gaba da aiki don wanzar da hadin kai, zaman lafiya, da ci gaban Najeriya, tare da bayar da shawarwari masu kyau game da magance matsalolin kasa.
Ya karfafa masa gwiwa kan ya ci gaba da tsayawa tsayin daka a bada gudummawarsa ga Najeriya yayin da yake yi masa fatan karin shekaru masu yawa na zaman lafiya, kariyar Allah, da koshin lafiya.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa an haifi Tinubu a ranar 29 ga Maris, 1952, a Legas.
KU KARANTA: Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah
A wani labarin daban, Shugaban jam'iyyar Bola Tinubu, ya yaba da jihar Kano cewa ita ce jihar da tafi kowacce jiha zaman lafiya a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.
Tinubu ya fadi haka ne a taron bikin maulidinsa na karo na 12 da aka gudanar a jihar Kano don tunawa da ranar haihuwarsa da cikarsa shekaru 69 a duniya.
sohon Gwamnan na Jihar Legas ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje game da nasarorin da ya samu musamman a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa.
Asali: Legit.ng