Zanga Zanga Ta Barke kan Soke Takarar Atiku a 2027, an Jero Bukatu

Zanga Zanga Ta Barke kan Soke Takarar Atiku a 2027, an Jero Bukatu

  • Masu zanga-zanga sun bukaci a fitar da sahihin kwafin hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke kan shugabancin ADC
  • Kotun ta soke shugabancin jam’iyyar karkashin Sanata David Mark tare da rushe dukkan matakan da shugabancin ya dauka
  • Masu zanga-zangar sun yi zargin jinkirin fitar da kwafin hukuncin da kokarin hana Atiku daukaka kara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wasu magoya bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun gudanar da zanga-zanga a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Masu zanga-zangar sun bukaci kotun ta fitar da sahihin kwafin hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke, wanda ya soke takarar Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

An yi zanga-zanga saboda Atiku
Atiku Abubakar na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Masu zanga-zanga sun mamaye kotu

Tashar Channels tv ta ce a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 masu zanga-zangar sun gabatar da koke a kotun, inda suka nuna rashin jin daɗinsu kan jinkirin fitar da kwafin hukuncin.

Kara karanta wannan

INEC ta yi magana kan fito da takardun Tinubu da soke takarar Atiku a zaben 2027

Sun yi zargin cewa jinkirin mika sahihin kwafin hukuncin ga lauyoyin Atiku wata dabara ce ta hana shi amfani da hakkinsa na daukaka kara.

Hukuncin kotu kan shugabancin ADC

A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya kori shugabancin jam’iyyar ADC karkashin Sanata David Mark.

Kotun ta kuma soke dukkan matakan da shugabancin ya dauka a madadin jam’iyyar, ciki har da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC.

Kotun ta bayyana kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar karkashin Sanata Mark a matsayin wanda bai dace da doka ba.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ADC na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar kan yadda kwamitin Sanata Mark ya karɓi ragamar shugabancin jam’iyyar.

Dalilin da ya sa Nafiu Bala ya kai ƙara

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito bayan shekaru 5, kotu ta sallami wanda ake zargi da kashe matarsa a Kano

Nafiu Bala ya bayyana cewa bayan tsohon shugaban ADC na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, ya yi murabus, shi ne wanda ya cancanci karɓar shugabancin jam’iyyar.

Ya kalubalanci tsarin da aka bi wajen kafa kwamitin da Sanata David Mark ke jagoranta, yana mai cewa bai dace a yi watsi da haƙƙinsa na shugabancin jam’iyyar ba.

Kafin hukuncin kotun, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta riga ta wallafa sunan Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.

Atiku ya kuma zaɓi tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da shi.

Za su kai ƙorafi ofishin jakadancin Amurka

Bayan gabatar da ƙorafinsu a kotun, masu zanga-zangar sun bayyana cewa za su kai irin wannan koke ofishin jakadancin Amurka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sun ce za su nemi waɗannan hukumomi su shiga tsakani kan abin da suka bayyana a matsayin tauye wa Atiku damar amfani da haƙƙinsa na ɗaukaka ƙara.

Masu zanga-zangar sun dage cewa ya kamata a fitar da sahihin kwafin hukuncin cikin gaggawa domin lauyoyin Atiku su samu damar bin matakan shari’a da suka dace.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya sake taso Atiku a gaba duk da nasara a kotu

Magoya bayan Atiku sun yi zanga-zanga a Abuja
Taswirar babban birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Atiku zai dawo da tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya sake jaddada cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.

Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC ya ce matakin zai taimaka wajen sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya da kuma rage musu nauyin tsadar man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng