Kungiyar Yarbawa ta yi Allah wadai da ziyara da kuma gudunmawar da Tinubu ya bayar a jihar Katsina

Kungiyar Yarbawa ta yi Allah wadai da ziyara da kuma gudunmawar da Tinubu ya bayar a jihar Katsina

- Wata kungiya a kudu maso yamma ba ta yi farin ciki da matakan Asiwaju Bola Tinubu na kwanan nan ba

- Kungiyar ta yi Allah-wadai da tallafin da Tinubu ya bayar kwanan nan ga wadanda gobara ta shafa a Katsina, tana mai cewa duk na ganin ido ne kawai

- A cewar kungiyar, wannan ba shine karo na farko da shugaban APC din ke cin amanar mutanensa ba domin neman saukakar siyasa a arewacin Najeriya

Wata kungiyar kudu maso yamma, Omoluabi Coalition ta yi Allah wadai da ziyara da gudummawar da tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya bayar ga wadanda gobara ta shafa a wata kasuwa a jihar Katsina.

A cewar wata sanarwa da kungiyar ta aika wa Legit.ng a ranar Alhamis, 25 ga Maris, kuma da sa hannun shugabanta, Seye Karounwi, tace matakin da jigon na APC ya dauka duk na ganin ido ne kawai.

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

Kungiyar Kudu maso Yamma ta yi Allah wadai da ziyara da kuma gudunmawar da Tinubu ya bayar a jihar Katsina
Kungiyar Kudu maso Yamma ta yi Allah wadai da ziyara da kuma gudunmawar da Tinubu ya bayar a jihar Katsina Hoto: @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Asiwaju Tinubu ya kawar da kai daga irin wannan rikicin a Kasuwar Sasha da ke Ibadan, jihar Oyo ko kuma gobarar da ta tashi kwanan nan a Kasuwar Akesan da ke cikin garin na Oyo, amma ya yi tsalle zuwa jihar Katsina don tausayawa wadanda lamarin ya rutsa da su kuma ya zama mai kula da' yan'uwansa.

"Mun yanke shawarar cewa manufar ziyarar Asiwaju Tinubu zuwa Katsina duk siyasa ce, kuma ba ta da wata alaka da taimakon jama'a."

A baya mun ji cewa Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, ya caccaki babban jigo a jam'iyyar All Progressives Congress APC, Bola Tinubu, kan ziyarar da ya kaiwa wadanda gobara ta yiwa illa a Katsina.

Omokri ya yi Alla-wadai da Tinubu kan yadda ya tsallake mutanen da gobara ta lashe dukiyansu a kasuwannin kudu maso yamma amma ya baiwa na Katsina gudunmuwar N50m.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa muka ce wajibi ne a bar dalibai mata su sanya Hijabi a makarantu, gwamnan jihar Kwara

Omokri ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita ranar Laraba jim kadan bayan ziyarar Tinubu jihar Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel