Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

- Hukumar JAMB ta shirya hanyoyin yin rijista don jarabawarta ta UTME na 2021

- Daliban da za su yi zaman zana jarabawar UTME din za su bukaci lambar shaidar zama dan kasa wato NIN

- Haka kuma akwai bukatar su mallaki adireshin e-mail nasu na kansu domin samun bayanai daga hukumar jarabawar

Hukumar Jarabawar Shiga Jami'a (JAMB) ta shirya hanyoyin yin rijista don jarabawarta ta UTME na 2021 a ​​ranar 8 ga Afrilu.

Hukumar ta ce tsarin zai gudana har zuwa 15 ga watan Mayu, 2021. JAMB ta kuma bayyana cewa lallai za bukaci lambar shaidar zama dan kasa (NIN) don yin rajista.

A cewar hukumar jarabawar, babu wani karin lokaci da zata yi wajen siyar da fom din UTME ko kuma na masu neman shiga aji biyu kai tsaye wato DE.

Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021
Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace mutane 4 a Abuja, sun nemi a biya N200m kudin fansa

Hukumar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da jarabawar ta na mock a ranar Juma’a, 30 ga watan Afrilu ga masu sha’awa yayin da UTME za ta fara daga ranar 5 zuwa 19 ga Yuni, jaridar TheCable ta ruwaito.

Shin kana shirin rubuta jarabawar JAMB gabanin shiga jami’a? Ga yadda ake shiga tsarin rubuta jarabawar UTME 2021 daga ranar 8 ga watan Afrilu.

Yadda ake shiga jarabawar UTME 2021

Ka samu ingantaccen adireshin e-mail: Da wannan, zaka iya aikawa da samun bayanai daga hukumar jarabawar.

Samu lambar NIN dinka: Idan baka da NIN, zaka bukaci mallakar daya.

Bayan haka, sai ka ƙirƙiri bayananka na JAMB: Tun ma kafin ka siya fom. Bayan rajista, zaka yi amfani da wannan wajen duba sakamakon ka ta yanar gizo idan ya fito, bincika matsayin samun gurbin karatu, ko kuma ka fitar da kwafin takardar samun gurbin karatunka.

Duba manhajar Jamb: Kafin kayi rijistar jarabawar UTME 2021, wani abin da yakamata kayi shine bincikar cancantar ka. Ana bayar da wannan bayanin ne akan adireshin yanar gizon hukumar jarabawar.

KU KARANTA KUMA: Dan Allah ka farka, kasar nan na wargajewa - Baba Ahmed ga Buhari

Daga nan, ci gaba da siyan fom din rijistar JAMB na 2021 a bankuna

Bayan wannan, kana iya zuwa kowane cibiyar yin gwajin yanar gizo wato CBT da keɓaɓɓun bayanankua da lambar bayanan ka.

A wani labarin, wani matashi ɗan kimanin shekara 35 ɗan asalin jihar Kano dake Arewa maso gabas ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa

Matashin mai suna Aminu Sa'idu yace ya shirya tsaf domin tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa na shekarar 2023.

Aminu Sa'idu ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa zai tsaya takarar ne saboda dokar ƙasa da tace 'Ban yi ƙanƙanta da tsayawa takara ba'.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel