Tinubu ya tsallake mutanen da gobara ta shafa a Legas da Oyo, amma ya baiwa na Katsina N50m: Omokri

Tinubu ya tsallake mutanen da gobara ta shafa a Legas da Oyo, amma ya baiwa na Katsina N50m: Omokri

- Gudunmuwar N50m da Tinubu ya baiwa mutan Katsina ya janyo cece-kuce

- Yayinda wasu ke ikirarin siyasa ne, wasu sun caccaki jigon na APC

- Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina ranar Laraba don jajantawa mutanen da gobara ya shafa

Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, ya caccaki babban jigo a jam'iyyar All Progressives Congress APC, Bola Tinubu, kan ziyarar da ya kaiwa wadanda gobara ta yiwa illa a Katsina.

Omokri ya yi Alla-wadai da Tinubu kan yadda ya tsallake mutanen da gobara ta lashe dukiyansu a kasuwannin kudu maso yamma amma ya baiwa na Katsina gudunmuwar N50m.

Omokri ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita ranar Laraba jim kadan bayan ziyarar Tinubu jihar Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yace, "Bola Tinubu, wanda bai kai ziyara ko bada gudunmuwan ko kwabo guda ga wadanda rikicin kasuwar Shasha ko gobarar kasuwar Ijesha a Legas ba, amma yau ya bada N50m ga mutanen da gobarar kasuwar Katsina ta shafa."

Tinubu bai bada gudunmuwa ba lokacin:

Gobarar kasuwar Ijesha a Legas (17 ga Junairu 2021)

Gobarar kasuwar Alade a Legas (26 ga Junairu 2021)

Gobarar kasuwar Sabo a Oyo (Maris 4, 2021)

Amma ya badda N50m ga na gobarar kasuwar Katsina, shin mutane kudu maso yamma ba mutane bane?"

DUBA NAN: Dattawan Arewa sun ba Gwamnatin APC satar-amsa 3 domin magance matsalar tsaro

Tinubu ya tsallake mutanen da gobara ta shafa a Legas da Oyo, amma ya baiwa na Katsina N50m: Omokri
Tinubu ya tsallake mutanen da gobara ta shafa a Legas da Oyo, amma ya baiwa na Katsina N50m: Omokri Hoto: UGC
Asali: UGC

DUBA NAN: Haske Yadawo a Maiduguri Bayan Wata Biyu da 'Yan Boko Haram suka saka garin a Duhu

Ranar Laraba, Tinubu ya kai ziyarar ban jaje ga yan kasuwan jihar Katsina tare da gwamnan jihar, Aminu Bello Masari.

Yayin jajanta musu, Tinubu ya ce jama'a su cigaba da kasuwancinsu duk da asarar da akayi.

Ya bayyanawa manema labarai cewa ya kai wannan ziyara ne domin jajantawa wadanda wannan abu ya shafa, gwamnan, da kuma al'ummar jihar Katsina gaba daya.

Tinubu ya jaddada cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin yan Najeriya.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel