Dalilin da ya sa muka ce wajibi ne a bar dalibai mata su sanya Hijabi a makarantu, gwamnan jihar Kwara
- Bayan makonni ana rikici, gwamnan jihar Kwara ya yi furuci kan lamarin Hijabi
- A cewar gwamnan, tuni akwai kulalliya tsakanin bangarorin biyu a jihar
- An bude dukkan makarantun da aka rufe sakamakon rikicin Hijabi a jihar Kwara
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman Abdulrazaq, ya yi bayani kan dalilin da yasa gwamnatinsa ta tsaya kan bakanta cewa wajibi ne a bar dalibai mata su sanya Hijabansu a makarantun Mission.
Gwamnan ya ce sun yanke shawaran haka ne bayan kwana da kwanaki suna tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Yace: "Mun yanke shawaran ne saboda jjin dadin al'umma gaba daya."
A jawabin da yayi ranar Talata, gwamnan yace: "Na fahimci tashin hankalin da ya faru tsakanin Musulmai da Kirista."
"Bayan zama da tattaunawa da kuma sauraron ra'ayoyin shugabannin bangarorin biyu a makonni hudu da suka gabata, na yi imanin cewa akwai dadadden kiyayya da ya zama wajibi a shirya da juna."
"Ina tabbatarwa mutan jihar Kwara cewa zamu dauki dukkan matakan da ya kamata wajen kwantar da kuran."
"Daga yanzu, muna bukatar da shugabannin Islama da Kirista su rika kalaman hada kan al'umma da yada soyayya da kuma ganin girman juna."
KU KARANTA: Dattawan Arewa sun ba Gwamnatin APC satar-amsa 3 domin magance matsalar tsaro
KU KARANTA: Kotu ta jefa Baturen zabe kurkukun shekara 3 kan yiwa APC magudin zabe
A bangare guda, kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi kira ga majalisar dokokin tarayya ta dakatad da wani shiri da ake yi a majalisar wakilai na yunkurin halasta amfani da Hijabi a makarantu a fadin tarayya.
A jawabin da Sakatare Janar na kungiyar CAN, Joseph Bade Daramola, ya sake, ya yi gargadin cewa wannan doka bai kamata a wannan lokaci ba, Punch ta ruwaito.
Kungiyar Kiristocin ta kara da cewa halasta sanya Hijabi zai tayar da tarzoma a Najeriya.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng