Taƙaddama ta ɓarke a Majalisar Dattijan Ƙasar nan kan cewa Wata ƙaramar Hukuma a Arewa ta zarce Jihar Bayelsa
- Taƙaddama ta ɓarke a zaman majalisar dattijai na ranar Talata ya yin da aka kawo kudirin gina babbar cibiyar duba marasa lafiya ta ƙasa a karamar hukumar Mubi, jihar Adamawa
- Taƙaddamar ta fara ne daga lokacin da Sanata daga jihar Adamawa, Aishatu Binani ta kawo misalin cewa ƙaramar hukumar Mubi ta zarce jihar Bayelsa girma.
- Sai dai misalin be ma Sanata Dickson daga jihar Bayelsa daɗi ba inda ya mike ya gargaɗe ta da tayi abinda ke gabanta ta daina saka jihar sa a ciki
Taƙaddama ta ɓarke a majalisar dattijan ƙasar nan a zamanta na ranar Talata lokacin da sanata Aishatu Binani ta jam'iyyar APC daga Adamawa ta bada misalin jihar Bayelsa a cikin jihohi marasa yawa.
KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Kaduna, sun sheke ma'aikacin lafiya da wasu mutum 3
Sanata Binani ta kawo wannan maganar ne ya yin da take ƙoƙarin kare kudirin data kai gaban majalisar kan buƙatar a gina cibiyar duba marasa lafiya a karamar hukumar Mubi, Adamawa.
Binani ta bayyana ma majalisar cewa, Mubi na da faɗin ƙasa da takai kimanin 506.2km2 wanda a cewarta karamar hukumar ta zarce jihar Bayelsa girma.
Ta kuma ƙara da cewa jihar Bayelsa ɗake da kananan hukumomi bakwai na da yawan jama'a kimanin 1,704,515.
Sai dai jawabin nata bai ma Sanata Seriake Dickson na jam'iyyar PDP daga Bayelsa dadi ba inda ya mike ya ƙaryata zancen nata.
Sanata Dickson ya ce girman jihar Bayelsa (wanda ya haɗa da faɗin kasa da kuma na ruwa) ya ninka girman wasu jihohin ƙasar nan sau uku.
KARANTA ANAN: An damke mai kaiwa yan bindigan Zamfara baburan da suke amfani da shi
Sanatan ya kuma gargaɗi Binani da ta gabatar da kudirinta ba tare da ta kawo misali da jihar Bayelsa ba, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya katse taƙaddamar sanatocin biyu inda ya gargaɗi Sanata Dickson da ya daina kawo abubuwan da basu da alaƙa da kudirin.
Daga ƙarshe kudirin na Aishatu Binani ya tsallake karatu na farko bayan gudanar da zaɓe akansa.
A wani labarin kuma Abinda Makiyaya ke yi bai dace ba, ya zama wajibi a hanasu kiwo, Inji Ɗawisu
Tsohon na kusa da gwamnan jihar Kano , Salihu Tanko yakasai wanda aka fi sani da Ɗawisu yace abunda makiyaya keyi be dace ba.
A cewar Ɗawisu ya zama wajibi gwamnati ta hana irin wanna kiwon da suke yi suna ma manoma ɓanna.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.
Asali: Legit.ng