Abinda Makiyaya ke yi bai dace ba, ya zama wajibi a hanasu kiwo, Inji Ɗawisu

Abinda Makiyaya ke yi bai dace ba, ya zama wajibi a hanasu kiwo, Inji Ɗawisu

- Tsohon na kusa da gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko yakasai wanda aka fi sani da Ɗawisu yace abunda makiyaya keyi be dace ba.

- A cewar Ɗawisu ya zama wajibi gwamnati ta hana irin wanna kiwon da suke yi suna ma manoma ɓanna

- Ya bayyana cewa irin waɗannan abubuwan sune maƙasudin farawar kashe-kashe tsakanin makiyaya da manoma.

Salihu Yakasai (wanda aka fi sani da Ɗawisu), tsohon mai taimakawa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa bazai yuwu abar makiyaya suna kiwo a buɗe ba, wajibi ne a hana su.

KARANTA ANAN: Shugaban kasa Buhari zai jagoranci bikin Maulidin Jagoran APC, Tinubu na 2021

Yakasai ya faɗi wannan magana ne ya yin da yake maida martani kan wani bidiyo da aka saki a kafar sada zumunta.

Bidiyon ya nuna wata mata a jihar Ogun na kuka saboda shanu sun shiga gonar kayan lambun ta suna kiyo, su kuma fulanin dake kiwon sun tsaya suna kallo.

Da yake bayyana ra'ayinshi akan bidiyon Ɗawisu yace:

"Wannan bai dace ba kwata-kwata kuma yakamata ayi watsi da irin wannan rashin adalcin na makiyaya. Bai kamata a amince da irin kiyon da suke yi ba, ya zama wajibi a dakatar da su."

Abinda Makiyaya ke yi bai dace ba, ya zama wajibi a hanasu kiwo, Inji Ɗawisu
Abinda Makiyaya ke yi bai dace ba, ya zama wajibi a hanasu kiwo, Inji Ɗawisu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

"Irin wannan shine asalin abin da ke kawo tashin hankali da kashe-kashe tsakanin manoma da makiyaya a ƙasar nan kuma Allah kaɗai yasan iya inda wannan abun zai kai matuƙar aka barshi ya cigaba da faruwa. Kawai a hana kiwon kwata-kwata." inji yakasai.

KARANTA ANAN: Muna nan zuwa kanku, Shugaban sojin Najeriya ga Igboho da Dokubo

A watan da ya gabata, jaridar Punch ta ruwaito Kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, ya bayyana shirin da gwamnati ke yi na kafa dokar da zata hana irin wannan kiwon da makiyaya ke yi.

A cewar sa, sabuwar dokar da za'a kafa zata taimaka wajen magance faɗace-faɗace tsakanin manoma da makiyaya a faɗin jihar.

A wani labarin kuma Gwamnati Za Ta Iya Dena Biyan Tallafin Lantarki a Karshen 2021, In Ji Hadimin Buhari

Ahmed Zakari, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman ne ya sanar da hakan yayin wata taro a Abuja

Zakari ya ce dena biyan tallafin ba zai saka farashin lantarkin ya yi tsada ba muddin ana samar da isasshen lantarkin.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262