'Yan bindiga sun kutsa jihar Kaduna, sun sheke ma'aikacin lafiya da wasu mutum 3
- Miyagun 'yan bindiga sun kai hari kananan hukumomin Igabi da Jema'a na jihar Kaduna
- Kamar yadda aka gano, sun kashe rayuka hudu, daga ciki har da wani ma'aikacin lafiya
- 'Yan bindigan sun raunata wasu mutum uku wadanda a halin yanzu suke jinya
'Yan bindiga sun halaka wasu mutum hudu da suka hada da ma'aikacin lafiya daya a kananan hukumomin Igabi da Jema'a na jihar Kaduna a ranar Litinin, sun bar wasu da raunika daga harsashi.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, lamarin ya faru a kauyen Unguwan Lalle dake karamar hukumar Igabi da asibitin Niima dake kauyen Golgofa a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna, jami'an gwamnatin jihar suka tabbatar.
A wata takarda da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar, ya sanar da cewa tun farko 'yan bindigan sun yi yunkurin rufe titin Kwanar Tsintsiya dake babbar hanyar Kaduna zuwan Abuja, amma sojoji suka fattatakesu.
KU KARANTA: Fani Kayode ya musanta cin zarafin ma'aikatansa na cikin gidansa, ya garzaya gaban kotu
KU KARANTA: Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna
Aruwan yace, kamar yadda rahotannin suka nuna, yayin da 'yan bindigan ke kan hanyar komawa sansaninsu ne suka kai hari kauyen Unguwan Lalle kuma suka kashe Dayyabu Yarima, Dalhatu Ashiru da Suleiman Samatu.
Yace a wani mummunan lamarin, dakarun rundunar Operation Safe Haven sun ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai hari asibitin Niima dake kauyen Golofa, karamar hukumar Jema'a ta jihar a daren Litinin kuma suka kashe ma'aikaci daya tare da raunata wasu mutum 3.
"Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana rashin jin dadinsa tare da fatan mutuwa ta zama hutu da wadanda aka kashe, ya mika ta'aziyya ga iyalansu. Yayi fatan wadanda suka samu rauni su warke tare da komawa cikin koshin lafiya," yace.
A wani labari na daban, a jiya ne wasu dattawan arewa suka yi magana a kan abinda suka kwatanta da kokarin illatawa tare da raunata arewa ta hanyar nuna cewa dukkan abubuwa marasa dadi dake faruwa na da alaka da yankin kafin zuwan zaben 2023.
Dattawan karkashin kungiyar dattawan arewa (NEF) sun ce abubuwa miyagu dake faruwa a kasar nan sakamako ne na masu mulki da suka kasa baiwa 'yan Najeriya kariya.
A wata takardar da aka turawa Leadership a Abuja, Dr Hakeem Baba-Ahmed, daraktan yada labarai na kungiyar, yace NEF na zargin cewa dukkan abubuwan dake faruwa ana yinsu ne don birkita 2023.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng