An damke mai kaiwa yan bindigan Zamfara baburan da suke amfani da shi
- An samu gagarumin nasara wajen yaki da yan bindigan da suka addabi Arewacin Najeriya
- Jami'an yan sanda sun damke mutumin da ke kaiwa yan bindigan babura
- An damke mutumin a Kano inda yake kaiwa yan bindiga babura a Zamfara
Hukumar yan sandan jihar Kano ta damke wani mutumin kan zargin kaiwa yan bindiga Zamfara baburan da suke amfani da shi.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa, ya bayyanawa BBC Hausa cewa an damke mutumin ne yayinda yake sayan baburan da yake shirin kaiwa jihar Zamfara.
Yayinda aka kaddamar da bincike, mutumin ya amda laifin sayarwa yan bindiga babura kimanin 100 a farashin N600,000 kan kowani guda.
"Yana sayar da babur Honda ACE 125, wacce aka fi sani da Boko Haram, wacce gwamnatin jihar Zamfara ta haramta amfani da ita. Suna canza kwalin a nan Kano sai su kai wa yan bindiga a Zamfara inda suka hadawa," Kiyawa yace.
"Mun damkeshi da babura biyu. Ya canza kwalayen kuma ya shirya kaisu Zamfara."
DUBA NAN: 'Yan bangan Amotekun sun sake kame wasu shanu sama da 300
KU KARANTA: Bidiyon Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yana nuna kwarewarsa a harkar rawa
A bangare guda, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a ranar Litinin ya bayyana cewa jihar Kano ta fi kowace jiha tsaro a Najeriya bisa matakan da gwamnatinsa ke dauka.
Ya yi alhinin matsalar rashin tsaro a Najeriya, musamman na karshen makon da ya gabata inda aka kaiwa gwamnan Benue, Samuel Ortom, hari.
The Nation ta rahoto Ganduje ya yi wannan jawabi bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng