Gwamnatin Najeriya roki 'yan kasa su daina amfani da robobi

Gwamnatin Najeriya roki 'yan kasa su daina amfani da robobi

- Gwamnati a Najeriya ta bukaci 'yan kasar su rage ko daina amfani da robobi a fadin kasar

- Wannan wani yunkuri ne na kare tsaftar muhalli da kuma rage hadarin gurbatar muhallin

- Tuni wasu jihohi a Najeriya suka dauki wannan magana suka fara gudanar da shirin ragewar

Gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan kasar su daina amfani da robobi su koma amfani da abubuwa masu saurin narkewa domin rage illolin da robobin ka iya haifarwa ga muhalli, BBC ta rahoto.

Mataimakin shugaban hukumar da ke kare muradan masu sayayya Barrister Babatunde Irukera ya ce tuni wasu jihohin irinsu Kano da Legas suka rungumi wannan tsarin na yadda za su rage amfani da robobi da yadda kuma za a rika sake amfani da robobin da aka yi amfani da su a baya.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da haramtacciyar matatar mai a Abia

Gwamnatin Najeriya roki 'yan kasa su daina amfani da robobi
Gwamnatin Najeriya roki 'yan kasa su daina amfani da robobi Hoto: greenpeace.org
Asali: UGC

An fara tattaunawa ne kan komawa amfani da abubuwan da ba su da illa ga muhalli dalilin ranar yancin masu sayayya ta duniya ta 2021, wadda aka yi wa taken "kawo karshen sharar robobi".

Gwamnatin za ta shigo da wasu shirye-shirye kan yadda za a rage amfani da robobi a kasar domin rage hadarin da sukan iya haifarwa.

KU KARANTA: APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni

A wani labarin daban, Gwamnatin Tarayya ta tura Rundunar Taimakon Gaggawa zuwa Jihar Kano don gano abin da ke boye na rashin lafiya tare da kula da wadanda suka kamu a cikin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Darakta-Janar na Cibiyar hana yaduwar Cututtuka ta Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin a taron hadin gwiwa na kasa da aka yi game da Kwamitin Shugaban kasa kan Korona.

Rahotanni sun ce mutane hudu sun mutu tare da wasu sama da 200 da suka kamu da wannan bakuwar cutar da aka tabbatar a kananan hukumomi 13, ciki har da kananan hukumomi takwas na birnin jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel